WHO ta ayyana dokar ta baci kan Coronavirus

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana cutar coronavirus a matsayin babbar barazar lafiya a duniya.
Annobar cutar coronavirus wadda ta yi ajalin sama da mutum dari a kasar China na ci gaba da yaduwa a wasu kasashe.
''Babban dalilin shi ne abin da ke faruwa a wasu kasashe bayan China," inji babban jami'in WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, a lokacin da yake sanar da 'yan jarida game da matakin a birnin Geneva.
Ya ce damuwar ita ce cutar na iya yaduwa zuwa kasashen da bangarensu na lafiya ke da rauni.
Mutum 170 annobar ta kashe a China ya zuwa yanzu.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutum 98 sun kamu da cutar a wasu kasashe amma ba a samu mutuwa ba.
An samu mutum takwas da kamuwa da cutar daga wasu mutane a Jamus da Japan da Vietnam da Amurka.
Ghebreyesus ya kwatanta barkewar cutar a matsayin wanda ba a taba samun irinta ba, wanda kuma aka tunkara fiye da a kowane lokaci.
Ya yaba wa China bisa daukar manyan matakan hana yaduwar cutar.
Wakilin BBC na harkar lafiya James Gallagher ya ce a yanzu WHO za ta iya tallafa wa kasashe matalauta da masu matsakaicin tattalin arziki wajen karfafa sanya ido da suke yi a harkar lafiya, sannan da taimaka musu wajen shirin ko ta kwana.











