Shin takunkumin kariya zai hana yaduwar kwayoyin cuta?

Woman wearing a surgical mask

Asalin hoton, Getty Images

Daya daga cikin hotunan da ake gani a lokacin da aka samu barkewar cuta shi ne mutane sanye da takunkumin kariya wato facemask a Turance.

Yin amfani da takunkumin domin kare kai daga abu ne da mutane ke yi a kasashen duniya da dama, musamman a China - inda aka samu barkewar cutar coronavirus, inda anan ma mutane ke sanya takunkumin kariyar domin kare kai daga gurbatacciyar iska.

Masana ilimin kwayoyin cuta na shakku game da tasirin takunkumin kariyar ga kamuwa da cututtukan da ke yaduwa ta iska.

Amma akwai bayanai da ke nuna cewa sanya takunkumin kariyar zai iya taimakawa wajen rage yada cutar.

An fara gabatar da takunkumin kariyar a asibitoci a karshen karni na 18, amma mutane ba su fara amfani da su ba har sai da aka samu barkewar murar Spanish flu a 1919 da ta hallaka mutum sama da miliyan 50.

Dr David Carrington, na Jami'ar London ya shaida wa BBC cewa "yawan sa takunkumin kariyar da jama'a ke yi ba hanya ba ce ta kariya daga kwayoyin cuta ko kwayoyin cuta da ke yaduwa ta iska, wanda ta haka ne ake yada kwayoyin cuta saboda sun kasance ba su da abin tace iska kuma idanu a waje."

Amma za su iya taimakawa wajen rage yiwuwar kamuwa da kwayar cuta ta hanyar atishawa ko tari tare da samar da kariya ga yaduwar cutar daga hannu zuwa baki.

Wani bincike da aka yi a 2016 daga New South Wales ya ce mutane na taba fuskarsu kusan sau 23 cikin sa'a daya.

A crowd wearing surgical masks in China

Asalin hoton, Getty Images

Jonathan Ball, farfesan kwayoyin cuta a Jami'ar Nottingham ya ce "a wani bincike da aka yi a asibiti, takunkumin kariyar da ake sa wa a fuska yana da kyau wajen kare kamuwa da kwayar cuta."

Na'urar kara numfashi da ke da matatar iska an tsara su ne domin kare cututtuka masu yaduwa ta iska.

"Sai dai idan ka duba irin binciken da aka yi kan irin tasirinsu ga jama'a, bayanan ba masu gamsarwa ba ne - akwai kalubale wajen ajiyar takunkumin kariyar na tsawon lokaci," in ji farfesa Ball.

Dr Connor Bamford na cibiyar nazarin magunguna ta Wellcome-Wolfsonda ke Jami'ar Belfast, ya ce "aiwatar da matakan tsafta" shi ne abin da ya fi tasiri wajen kare kamuwa da kwayoyin cuta.

"Rufe baki a lokacin atishawa da wanke hannaye sannan kaucewa kai hannu baki kafin wanke su zai iya taimakawa wajen rage kamuwa da wata kwayar cuta ta numfashi," a cewarsa.

Hukumar kula da ayyukan kiwon lafiya ta Birtaniya NHS ta ce hanyoyin kare kai daga kamuwa da kwayoyin cuta su ne:

  • Wanke hannu akai-akai da ruwan dimi da kuma sabulu
  • Kaucewa taba idanu da hanci
  • Kawan tsafta da zama cikin tsaftataccen muhalli

Dr Jake Dunning, shugaban kula da cututtuka masu yaduwa a sashen kula da lafiyar al'umma a Birtaniya ya ce "duk da cewa akwai wasu da ke ganin sanya takunkumin kariyar na fuska yana da alfanu, babu wasu hujjoji kwarara cewa yana kare mutum daga kamuwa da kwayoyin cuta."

Ya ce dole sai an sa takunkumin kariyar yadda ya kamata tare da sauya shi akai-akai idan har ana son ya yi aiki yadda ya kamata.

"Bincike ya kuma nuna cewa amfani da wadannan shawarwari na raguwa idan aka sanya takunkumin kariyar na tsawon lokaci," a cewarsa.

Dr Dunniny ya ce idan har mutane sun damu, ya kamata su mayar da hankali kan kula da tsaftar su da kuma wanke hannu.