Tambayoyi da amsa kan Cutar Coronavirus

Asalin hoton, EPA/WU HONG
Zuwa yanzu cutar Coronavirus ta kashe fiye da mutane 80 a China da wasu kasashen duniya, kuma tana cigaba da yaduwa.
Mahukunta sun rufe garin Wuhan inda can ne ta fara bulla kuma tafi tasiri.
Ana tunanin cewa cutar ta samo asali ne daga wata kasuwa da ake sayar da naman namun daji ba bisa ka'ida ba.
Mahukunta a Birtaniya sun zage dantse wajen aiwatar da bincike a kan masu zuwa daga China don gudun abin da ka je ya zo.
Wakilan BBC kan lafiya da kuma kimiyya Michelle Robers da James Gallagher, sun amsa muhimman tambayoyi a kan ita wannan cuta mai saurin kisa ta Coronnavirus.
Shin zaa iya safarar kwayar cutar ta hanyar safarar wasu kayayyaki da aka sayo daga Wuhan zuwa Birtaniya?
Babu wata shaida da ta nuna hakan na tattare da hadari. Wasu cututtukan ciki har da Coronavirus wadanda ke haifar da zazzabi na iya yaduwa ne ta hanyar mutanen da ke fyace hancinsu musamman in iska na kadawa.
Ba a bayyana cewa cutar na yaduwa ta hanyar safarar kayayyaki ba, idan ma nan gaba bincike ya nuna hakan, za a jefa ayar tambaya a kan ko safarar kayayyaki daga kasa zuwa kasa na iya zama hadari.
Sai dai kwayoyin cuta masu saurin kamuwa na rayuwa ƙasa da sa'o'i 24 a waje da jikin mutum duk da cewa norovirus (ƙwayar ciki mai zafi) na iya wuce watanni a waje da jikin mutum.
A kashin gaskiya abu mafi tabbatuwa kawai shi ne ana iya kamuwa da cutar ne idan aka cudanya da mai dauke da ita, abinda masana lafiya suka ce kenan.
Akwai wani dalili da ya nuna cewa ana sake samun bullar cutar daga China?
Eh, akwai mutane da yawa da ke rayuwa kusa da dabbobi.
Ba shakka ita ma wannan cuta ta Coronavirus ta samo asali ne daga jikin dabbobin, musamman ma macizai, da Jemagu da damo.
An gano cewa an samu bullar cutar ne a karon farko a wata kasuwa da ake sayar da naman dabbobin dawa da ake sayar da irin wadancan dabbobi da muka fada a sama.
Babban abin shawara kawai shi ne mutane su rika takatsantsan da abubuwan da suke saya daga kantuna da kuma kwalam da makulashe na nama.
Kasancewar jirage uku ne ke tashi daga Wuhan zuwa London a kowanne mako, ko ya kamata mu rika toshe fuskokinmu da hancinmu?
A'a, domin kuwa babu rahoton bullar cutar a Birtaniya har ya zuwa yanzu, kai hatta ma ciwon gabobi a yanzu ya fi shi zama barazana.
Menene banbancin yaduwar cutar idan aka kwatanta da yadda sauran cututtukan ke yaduwa?
Abu ne mai wuya a iya gane yadda take yaduwa.
Yawancin irin wadannan sabbin cututtukan dama na nan a gari, amma daya daga ciki da aka iya ganowa ita ce wannan da ta bulla a China.
Babu cikakkun bayanai game da karuwar yaduwar ta.
Akwai wani abu da zamu iya yi ne don kare kai
Babu wani magani da zuwa yanzu aka samar don kiyaye cutar.
Likitoci ne za su yi kokarin gano ta a duk lokacin da aka samu rahoton bullar ta, har ma su kebance mutanen da ba su kamu da ita ba daga cikin wadanda suka kamu don gudun abinda ka je ya zo.
Akwai damar yin riga-kafin kamuwa da Coronnavirus?
Zuwa yanzu babu wani maganin kare kai daga kamuwa da ita wannan cuta, amma masu bincike sun dukufa domin tabbatar da samun shi.
Cuta ce da ba'a taba samun irin ta ba a baya, don haka likitoci na da jan aiki a gaban su, kamar kaine ace kana yaki da abin da baka sani ba.
Zaa iya tunnain cewa wadanda suka je China a 'yan watannin baya sun kamu da cutar alal misali a watan Octoba?
To an dai samu rahoton farko na bullar cutar ne a watan Disamba a Wuhan.
Abu ne mai wuya a iya gano ko ta jima da bulla ko akasin haka, amma cuta na kwashe makwanni biyu ne kafin ta yi tasirin da za ta bayyana har a ganta karara a jikin mutum.
Masana sun yi amannar cewa da farkon fari an dauki cutar ne daga cikin dabba.
Shin filayen jiragen saman Birtaniya na shirin soma tantance matafiya daga China musamman wadanda ke rungumar makusantan su da sunan murnar isowa a wannan makon?
Ana irin wannan bincike a yawancin filayen jiragen sama na duniya idan matafiya suka zo daga Wuhan.
An ajiye na'urorin binciken cututtuka na musamman don irin haka.

Asalin hoton, Getty Images
An sallami yawancin mutanen da ake tunanin sun kamu da cutar daga aibiti, kenan wannan na nufin cewa cutar bata da wani hadari sosai kenan?
A kashin gaskiya Coronavirus curin ƙwayoyin cuta ne waɗanda ke haifar da cututtuka musamman murar kwana da kwanaki, daga nan kuma sai jiki ya tsananta tafi-tafi haka al'amarin zai ci gaba.
Idan mai fama da cutar ya murmure, babu barazanar zai iya yada ta ga jama'a kuma tunda ya samu sauki.
Wacce dabba ce ƙwayar Corona ta fito?
Masana suna aiki don nemo asalin.
Tabbatattuwar shawarwari don hana kamuwa da cuta suna aiki. Wadannan sun hada da
- Wanke hannu yau da kullun
- Rufe bakin da hanci yayin tari da hancin
- Dafa abinci sosai da ƙwai
Ka guji kusanci da duk wanda ke nuna alamun cututtukan numfashi kamar tari da zazzabi.















