Kannywood ta shiga jerin sabbin kalmomin Kamus na Oxford

Asalin hoton, Getty Images
Kalmar Kannywood wacce ake nufi da masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake yi a arewacin Najeriya ta samu shiga cikin kamus din Turanci na Oxford Dictionary da ake wallafa shi a Birtaniya.
Kamfanin da ke wallafa kamus din ne ya wallafa hakan a shafinsa na intanet a ranar Talata.
Kalmar ta Kannywood tana cikin jerin kalmomin Turancin Najeriya 10 da suka sake samun shiga cikin kamus din a karo na farko.
An kirkiri kalmar Kannywood da kuma fara amfani da ita a shekarar 2002, kuma ta samo asali ne daga Hollywood wato masana'antar fina-finan Amurka, sai kuma aka samu Nollywood, wato sunan da ake kiran masana'antar fina-finan Najeriya da aka kara cikin Kamus na Oxford a 2018.
Yawancin wadannan karin da aka samu ko dai aron kalmomi ne daga yarukan Najeriya ko kuma wata hanya ta daban, da 'yan Najeriya ke yi wajen sauya kalmomi da aka fara amfani da su a tsakiyar karni na 20, yawanci a shekarun 1970 da kuma 1980.
Wani abu daya da zai ba ku sha'awa a jerin kalmomin da aka ara ko aka sauya su suka zama Turanci su ne irin abincin da ake sayarwa a kan titunan Najeriya.
Misali, kalmar "bukka" an aro ta ne daga yaren Hausa da kuma Yoruba aka kuma fara amfani da ita a shekarar 1972, kalmar na nufin gidan sayar da abinci mai sauki da ke gefen titi.
Wata kalmar da aka ara daga ire-iren gidajen sayar da abinci wanda aka shaida a shekarar 1980 ita ce, "bukateria", wadda aka kara da "bukka da kuma kalmar Turanci -"teria" wato karshen kalmar "cafeteria".

Ra'ayin marubuciya Chimamanda Ngozi Adichie
Shaharriyar marubuciya 'yar Najeriya Chimamanda Ngozi Adichie ta kwatanta dangantakarta da Turanci, yaren da take amfani da shi wajen rubuce-rubucenta.
''Turancin da nake yi ya samo asali ne daga Najeriya ba kuma irin na Birtaniya ko Amurka ko na Australiya ba. Na dauki hakkin mallakar yaren Ingilishi.''
Haka kuma miliyoyin 'yan Najeriya irinta ke amfani da shi wajen sadarwa.
Mallakar Turanci a matsayin yaren da muke amfani da shi wajen sadarwa, 'yan Najeriya na ci gaba da bayar da muhimmiyar gudummawa ga Turanci a matsayin yaren duniya.
Marubuciyar ta bayyana cewa ''Mun yi karin haske kan gudunmawar da 'yan Najeriya suka bayar a wannan watan na Kamus din Oxford, yayin da wasu adadin kalmomin Turancin Najeriya ya samu shiga kamus din a karon farko.''
Kalmar da ma aka fi yi mata hikima ita ce ta "mama put", wadda aka fara amfani da ita a shekarar 1979, ta samo asali ne daga yadda masu sayen abinci a buka ke cewa: 'Mama zuba min'...
Wasu daga cikin sabbin kalmomin sun hada da:
- Mama put
- Okada
- Kannywood
- Guber
- Agric
- bukateria da sauran su.

Kalmar daga baya sai ta zama sunan da ake kiran masu sayar da abinci da ita baki daya - wanda ya karbi lambar yabo ta Nobel kan rubutun littafin wasan kwaikwayo, Wole Soyinka ya yi amfani da 'Mama put' a daya daga cikin littattafansa.
An fara amfani da kalmar 'Okada' shekaru 20 baya, kalma ce da ake kiran abin hawa kamar 'acaba' na haya da fasinjoji ke amfani da shi a matsayin sufuri.
Kalmar ta samo asali ne daga jirgin saman nan mai suna 'Okada Air' da ya taba aiki a Najeriya daga shekarar 1983 zuwa 1997, da kuma suna da jirgin ya yi wajen tafiya da saurin gaske amma fa cike da hatsari, kamar dai yadda 'acaba' din yake.

Asalin hoton, INSTAGRAM/@OFFICIAL_HAFSAIDRIS20
Wasu daga cikin kalmomin Turancin Najeriya kadan da aka samu karinsu cikin kamus din su ne kalmomin Turanci da aka gutsure karshensu.
Kalmomin da suka fi tsufa cikin karin kalmomi da aka samu wadanda asali ta Najeriya ce ita ce 'next tomorrow' - wato yadda 'yan Najeriya ke fadin 'jibi' a Turance a maimakon 'the day after tomorrow'.
An fara amfani da ita ne a rubuce da Turanci a matsayin 'suna' a shekarar 1953, sai kuma a matsayin 'aikatau' a shekarar 1964.












