Shugaba Buhari ya tafi Birtaniya don halartar taron zuba jari

Lokacin karatu: Minti 1

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi birnin Landan a ranar Juma'a domin halartar taron zuba jari na Birtaniya da Afirka.

Mataimaki ga shugaba Buhari kan yada labarai, Buhari Sallau ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa tuni shugaban ya tashi daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe International da ke Abuja.

Tun da farko dai fadar shugaban Najeriyar ce ta sanar da tafiyar shugaban a shafinta na Twitter a ranar Alhamis.

Taron wanda za a yi ranar 20 ga watan Janairun nan, ya zama tafiyar Buhari ta farko zuwa wani wuri a shekarar 2020.

Firai Minsitan Birtaniya Boris Johnson ne zai zama mai massaukin baki na taron, wanda ake sa ran zai hado kan shugabannin kasashen Afirka da manyan 'yan kasuwa na duniya.

Ana fatan taron zai samar da sabbin damarmakin kasuwanci da zuba jari da samar da ayyuka, wanda zai amfani nahiyar Afirka da Birtaniya.