Dole Buhari ya bar mulki a 2023 - PDP
Ku latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraron Sanata Umar Ibrahim Tsauri.
Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta bukaci Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya janye kalamansa na sabuwar shekara da ta ce ba lallai ba ne game da nanata aniyarsa ta "rashin tsayawa takara" a 2023.
Jam'iyyar ta PDP ta ce dole ce ta sa Shugaba Buhari nanata batun rashin son tsayawa takarar tasa domin kuwa ba shi da sauran zabi sai na barin mulki a karshen wa'adinsa .
A ranar Laraba ne dai yayin jawabin shiga sabuwar shekara, Shugaban ya sake fadin cewa ba shi da niyyar sake tsayawa takara a 2023.
To sai dai sakataren jam'iyyar mai hamayya ta PDP, Sanata Umar Ibrahim Tsauri ya ce kamata ya yi Shugaba Buhari ya daina nuna tamkar yana da wani zabi na ci gaba da mulki har bayan shekara ta 2023.








