Cikin Hotuna: Ziyarar Emmanuel Macron a Nijar

Ranar Lahadi ne Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kai ziyara kasar Nijar domin yin ta'ziyyar sojojin nan 71 da 'yan bindiga suka kashe.

Shugaba Mahamadou Issoufou da Emanuel Macron
Bayanan hoto, Shugaba Muhamadou Issoufou na Nijar da twkwaransa na kasar Faransa Emanuel Macron sun kai ziyara makabartar da aka binne sojojin Nijar da 'yan bindiga suka kashe
Shugaba Mahamadou Issoufou da Emanuel Macron
Bayanan hoto, Macron ya kai ziyarar ne a kan hanyarsa ta zuwa kasar Ivory Coast domin yin bikin Kirsimati tare da sojojin kasarsa
Shugaba Mahamadou Issoufou da Emanuel Macron
Bayanan hoto, Kasar Faransa ce tsohuwar uwar gijiyar Nijar, wadda ta yi wa mulkin mallaka shekara 61 da suka gabata
Shugaba Mahamadou Issoufou da Emanuel Macron
Bayanan hoto, Akwai daruruwan dakarun kasar Faransa a kasar ta Nijar, wadanda suke horarwa tare da taimaka wa wasu rundunonin sojan Nijar din
Shugaba Mahamadou Issoufou da Emanuel Macron
Bayanan hoto, Sai dai ziyarar tasa ta gamu da cecekucen daga wasu 'yan Nijar, inda suka ce ba sa maraba da shi sannan suka zargi Faransa da mara wa 'yan bindigar baya
Shugaba Mahamadou Issoufou da Emanuel Macron
Bayanan hoto, Wasu 'yan kasar ta Nijar, har wa yau, sun yi kiran da Faransa ta tattara komatsanta ta bar masu kasarasu