Mahara sun kashe sojojin Nijar sama da 70

Issoufou

Asalin hoton, Getty Images

Bayanai daga jamhuriyar Niger na cewa shugaban kasar, Mahamadou Issoufou ya katse ziyarar aiki da yake yi a kasar Masar domin nuna alhinin kisan sojojin kasar guda 73.

A ranar Talata ne dai wasu mahara suka hallaka sojojin Nijar din 73 tare da raunata wasu 12, yayin da wasu kuma suka bata a wasu hare-hare da ake zargin masu tayar da kayar baya da kai wa a wani sansanin sojin kasar, a yankin Tillabery da ke kan iyaka da kasar Mali.

Gwamnatin kasar ta ce an kai harin ne wanda ya kasance mafi muni a kasar ta Nijar tun 2015, a ranar Talata a garin Inates, wanda bai da nisa daga inda aka kashe sojojin Amurka hudu da na Nijar din biyar a harin kwanton-bauna shekara biyu da ta wuce.

A wata sanarwa da gwamnatin Nijar din ta fitar ta ofishin ministan tsaron kasar, ba ta bayyana yawan sojojin da rahotanni ke cewa sun bace ba a harin, amma ta sanar cewa su ma maharan, wadanda suka kai farmakin a kan babura da motocin yaki sun yi asarar rayuka da dama.

Babu dai wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai harin, wanda aka kai shi ranar ta Talata da yamma.

Sojojin Nijar a lokacin da shugaban kasar ke ziyartarsu

Asalin hoton, Others

Ko a watan Yuli ma an kai hari kan wannan sansani wanda ke kan iyaka da Mali, wanda a lokacin maharani suka kasha sojoji 18.

Masu sharhi kan al'amuran tsaro na cewa hare-haren na masu tayar da kayar baya a Nijar na kara ta'azzara.

Kungiyoyin mayaka masu ikirarin Jihadi wadanda suke da alaka da Al Qaeda da IS suna kai hare-hare a yankunan Nijar din da ke arewa, inda take da iyaka da Mali da Libya, yayin da kungiyar Boko Haram take da karfi a yankin iyakar kasar da Najeriya, a arewa maso gabas.

An kai wannan harin ne 'yan kwanaki kafin taron shugabanni da za a yi a Faransa wanda Emmanuel Macron zai karbi bakuncin shugabannin kasashen Afirka ta Yamma, domin tattauna batun tsaro a yankin.

A farkon makon nan gwamnatin Nijar din ta tsawaita dokar ta-baci a wasu yankunan jihohi 3 da ke karkashin dokar tun shekara biyu da ta wuce, da Karin wata uku, saboda yawaitar hare-haren masu ikirarin Jihadi.

Ayarin sojojin Nijar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Maharan sun kai hari ne da yamma a kan sojin na Nijar a kan babura da motocin yaki