Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Maudu'ai 12 da suka fi tashe a shafukan sada zumunta a Najeriya a 2019
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja Bureau
- Lokacin karatu: Minti 6
Shekara kwana, kamar yau aka shiga 2019 ga shi har ta kare. Sai dai BBC ba ta barin zarau sai ta tsinka!
Za mu tuna maku wasu muhimman abubuwa da suka dinga tashe a shafukan sada zumunta da muhawara ba, musamman wadanda aka dinga kirkirar masu maudu'i.
Ga kadan daga cikin wasu batutuwan da muka samu damar zakulowa.
#ArewaTwitter
Tun daga farkon shekarar 2019 ne maudu'in #ArewaTwitter ya fara tashe. Sai dai babu wanda zai bugi kirji ya ce shi ya kirkiri wannan maudu'i.
Kuma an yi ta amfani da shi a fadin Najeriya har zuwa karshen 2019, inda a duk lokacin da wata muhawara ta barke tsakanin 'yan Kudanci da Arewacin kasar sai maudu'in ya sake kunno kai.
Daga cikin manyan batutuwan da aka dinga amfani da maudu'in wajen tattauna su har da batun Rahama Sadau na baya-bayan nan.
An yi wa tauraruwar ca kan wata shiga da ta yi a bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta da kuma bikin bude Saudauz Home, inda ta cashe tare da mawakin Hausa Hip Pop Classiq.
Rahama ba ta bari kasuwar ta tashi ba sai da ta tofa tata, hasali ma da ita aka ci kasuwar tun daga farko, duk da cewa ita ba ta yi amfani da maudu'in na #ArewaTwitter ba.
Kamar yadda aka saba a shafin Twitter na Najeriya, daga baya mutane da dama sun yi ta amfani da maudu'in domin tallata hajarsu da kuma kasuwarsu.
#NigeriaDecides
Idan akwai wani batu da aka tattauna sosai a shafukan sada zumuntar Najeriya to yana bayan zabukan kasar da aka yi a watan Fabarairu da Maris.
Al'ada ce a mafi yawan kasashen duniya musamman masu yin Turancin Ingilishi, duk sanda za a yi zabe sai a fadi sunan garin ko kasar tare da mudu'in #Decides.
Kamar yadda kuka sani kuma Najeriya tana da kirarin cewa "9ja no dey carry last" (ba a barin Najeriya a baya).
An kirkiri #NigeriaDecides aka kuma ta yin amfani da shi sau dubun-dubata a watanni biyun da zabukan suka gudana.
#IamNorth
Wani maudu'in da ya yi tashe a lokaci guda da lokacin zaben shi ne na #IamNorth kuma ya samo asali ne bayan an fara bayyana sakamakon zaben.
Mafi yawan wadanda suka yi amfani da maudu'in 'yan Arewa kuma Hausawa domin mayar da martani ga zargin da abokan zamansu suka yi masu cewa su suka zabi gwamnatin Shugaba Buhari ganin cewa ya (Buhari) fi samun kuri'a mai yawa daga yankin.
A takaice dai hirar siyasa ce ta rikide zuwa ta kabilanci a wannan loikaci, inda 'yan Najeriya suka cashe wa junansu a Twitter.
Maudu'in ya dauki kwanaki yana tashe (a harshen shafukan sada zumunta). Da Hausa, #IamNorth yana nufin "ni ne Arewa".
Sanata Elisha Abbo
A farkon watan Yuli ne kuma Sanata Elisha Abbo ya shiga uku a Twitter sakamakon bidiyon da Premium Times ta wallafa yana falla wa wata mata mari mai jiran shagon sayar da kayan jima'i na roba a Abuja.
'Yan Najeriya, musamman mata, suka saka Sanatan a gaba har sai da ya bayar da hakurin abin da ya aikata, sannan kuma 'yan sanda suka gurfanar da shi a gaban kotu.
An kai kusan wata guda #ElishaAbbo yana tashe musamman saboda harzukar da 'yan Najeriya suka yi ganin cewa sanata ne da kansa ya aikata.
#NorthernYouthSummit
Taron da aka yi a garin Kaduna wanda kuma Aisha Falke, mamallakiyar shafin Northern Hibiscuss a Instagram, ta jagoranci gudanarwa, shi ne ya samu maudu'in #NorthernYouthSummit.
An gudanar da taron ne a watan Yuli, inda aka gayyaci 'yan gayu da 'yan boko da 'yan gwamnati daga Arewacin Najeriya.
Ba don komai aka gayyace su ba sai don nemo wa yankin mafita game da matsalolin tattalin arziki da yake ciki.
BBC na iya tunawa cewa Gwamna Nasir El-Rufa'i da Ali Nuhu da wasu sanannun fuskoki sun halarci taron - kai har da mawaka fa.
An yi ta amfani da maudu'in a dukkanin tsawon kwana kwana biyu (4 da 5 ga watan Yuli) da aka yi ana gudanar da shi.
#Dadiyata
Ko yanzu kuka bincika maudu'in #Dadiyata a shafukan sada zumunta ba za ku rasa ganin wanda ya yi amfani da shi ba a yau saboda irin kiraye-kirayen da mutane ke yi domin a saki Abubakar Idris Dadiyata.
In muka dan tuna baya, a watan Agusta ne wasu da ba a san ko su wane ne ba suka shiga gidan Dadiyata da tsakar dare suka yi awon gaba da shi.
Da yake Dadiyata dan jam'iyyar PDP ne darikar Kwankwasiyya, har yanzu 'yan jam'iyyar kan yi amfani da maudu'in su soki gwamnatin Kano da ta tarayya da zargin cewa su suka sace shi.
Kazalika, duk sanda aka kama wani dan fafutika akan tuno da Dadiyata sannan kuma a yi amfani da maudu'ai kamar: #FreeDadiyata, #WhereIsDadiyata, #WhoTookDadiyata.
Auren Buhari - #Busa2019
Kwatsam sai aka wayi gari a watan Oktoba da labarin cewa Shugaba Buhari zai yi wa abar kaunarsa Aisha kishiya. Saboda babu wanda yake son gulma ta wuce shi a soshiyal midiya, sai aka kirkiri maudu'in #Busa2019.
"Bu" tana nufin Buhari, ita kuma "Sa" din tana nufin Sadiya, wato Sadiya Umar Farouk - Ministar Ma'aikatar Jin-Kai da Bayar da Tallafi - wadda ita ce aka ce zai aura din.
Kusan kwana uku aka yi maudu'in yana tashe a Twitter da Instagram saboda, kamar a ko ina, labari irin wannan daga babban gida yana saurin kama kunnuwa.
#ZainabAliyu
Sunan Zainab Aliyu da kansa ne ya karade shafuka musamman Facebook da Twitter saboda kiraye-kirayen da 'yan Najeriya suka rika yi a watan Afrilu ga kasar Saudiyya da a saki baiwar Allahn.
Hukumomin Saudiyya sun zargi Zainabu Abu da safarar miyagun kwayoyi zuwa cikin kasarsu, amma 'yan Najeriya ba su amince da zargin ba kuma nan take maudu'in #ZainabAliyu ya bayyana.
Maudu'in ya sake farfadowa a watan Mayu bayan shaida wa BBC irin halin da ta shiga a cikin gidan yarin (Saudiyya cikin hawaye), bayan an sake ta.
#SexForGrades
Da wahala a daina amfani da wannan maudu'in na #SexForGrades a nan kusa saboda ba wai daidaikun miutane ne kawai ke amfani da shi ba, har da kafafen yada labarai.
Ba abin mamaki ba ne domin kuwa BBC ce ta bankado lalatar da wasu malaman jami'o'i ke yi da dalibai mata a Najeriya da Ghana domin ba su makin jarrabawa.
Sai da Maudu'in ya yi sama da kwana biyu yana tashe sannan kuma kusan a kullum sai wani ya yi amfani da shi, akasari ko an kama wani malami ko kuma wata ta zargi wani malamin. Haka dai.
#ArewaMeToo
#ArewaMeToo kamar wata lasifika ce da wasu mata daga Arewacin Najeriya suka yi amfani da ita domin fallasa cin zarafin da aka yi wasu daga cikinsu.
Maudu'in ya yi tashe sosai tun a watan Fabarairu, inda aka rika kiran sunayen mazaje tare da tona asiri ko kuma zarginsu da wasu laifukan lalata da cin zarafin mata.
Daya daga cikin wadanda suka kirkiro shi Fakhriyya Hashim, ta ce sun yi hakan ne domin taimaka wa wadanda ba su da yadda za su yi a ji koke-kokensu.
#BBNaija
Duk wanda bai taba ganin maudu'in #BBNaija ba a shafukan sada zumunta to wayarsa bva ta da amfani, ko dai ya jefar da ita ko kuma ya hakura da soshiyal midiya.
BBNaija shirin talabijin ne na-fili da ake gabatarwa a jihar Legas, a duk lokacin da aka yi wani abu na musamman a shirin sai maudu'in ya yi tashe.
Na baya-bayan nan shi ne na matashiyar nan Tacha, wadda aka kora daga shirin saboda saba wasu doki, in ji mahaukuntan shirin.
Tabbas #BBNaija yana cikin wadanda suka kowanne maudu'i tashe a shekarar baki dayanta.
#RahamaSadau
In aka ce Kannywood na tabbata idan Rahama Sadau ba ta zo ta daya a zukatanku ba to ba lallai ta wuce ta uku ba, kazalika a 2019 ma ba ta fasa tashe ba.
Ta yi tashe a lokuta daban-daban, daya lokacin da ta yi bikin ranar haihuwarta da kuma lokacin da kuma loakcin da ta bude wata cibiyar kasuwancinta mai suna Sadauz Home.
Sadau dai ta sha luguden cecekuce game da shigar da ta yi a lokutan bukukuwan, abin da ya sa ma #RahamaSadau ya karade shafuka a watan Nuwamba zuwa Disamba.