Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan sanda sun fara binciken Sanata Elisha Abbo
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fara binciken Sanata Elisha Abbo wanda ake zargin ya ci zarafin wata mata a kantin sayar da robobin jima'i a Abuja.
Mai magana da yawun rundunar Frank Mba ya shaida wa BBC cewa Babban Sufeton 'yan sandan kasar Muhammed Adamu ya bayar da umarnin a fara binciken dan majalisar dattawan.
'Yan Najeriya suna ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu tun bayan da kafar yada labarai ta Premium Times ta wallafa wani bidiyo mai tsawon minti 10 da ke ikirarin nuna sanatan yana dukan wata mata a cikin wani shago.
"'Yan sanda sun tuntubi matar kuma mun fara bincike, fatanmu shi ne mu tabbatar cewa an yi abin da ya dace. Za mu yi bincike sosai.
"Za mu duba komai da komai, za mu yi nazari a kan bidiyon, kuma a karshe za mu sanar da 'yan Najeriya abin da bincikenmu ya gano," in ji kakakin 'yan sandan.
'Bidiyon ba cikakke ba ne'
Sanatan ya shaida wa BBC cewa faifan bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta "ba cikakke ba ne" sannan abin ya kwana biyu da faruwa.
A wata hira da sashen Pidgin na BBC, ya ce abin da ya faru a bidiyon shi ne wata mata ce ta fara marinsa.
"Abin ya faru lokaci mai tsawo a baya kafin na zama sanata. Wata kanwata ce ta kira ni ta ce min na je shagon, inda na je na tarar da kawarta kwance a sume," in ji sanatan.
Ya ci gaba da cewa: "Bidiyon bai nuna cikakken abin da ya faru ba. Sun yanke wurin da kanwata take kwance a sume a shagon.
"Bayan na kira 'yan sanda da motar asibiti, sai na fita daga shagon, a nan ne kuma wata mace rike da littafin Baibul Mai Tsarki ta mare ni har sau uku. Wannan ne ya sa ni daukar matakin."
A karshe ya ce al'amarin ya faru ne a ranar 11 ga watan Maris na bana a wani shago da ke ginin Banex Plaza a Abuja.
'Ya kamata PDP ta dauki mataki a kansa'
Tuni dai wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar PDP, wadda Sanata Elisha Abbo ya lashe zabe a karkashinta suka fara tofa albarkacin bakinsu a kan lamarin.
Alhaji Atiku Abubakar, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar a babban zaben 2019, ya ce ya yi wa sanatan farin sani amma kamata matasan shugabanni irinsa su zama abin koyi.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya ce kamata jam'iyyar PDP ta dauki matakin ladaftarwa a kan sanatan.
"Ina shawartarsa da ya fito fili ya nemi afuwa sannan ya mika kansa ga 'yan sanda domin ya nuna dattako.
"Sannan kuma ina kira ga uwar jam'iyyarmu ta PDP da ta dauki matakin ladaftarwa a kansa, su ma 'yan sanda su tabbatar cewa doka ta yi aikinta."