Shekara 20 ta Vladimir Putin cikin hotuna 20

Shugaban Rashsa Vladimir Putin na jawabi a lokacin yakin neman zabe a watan Maris 2018

Asalin hoton, Getty Images

Vladimir Putin na shirin bikin cikarsa shekara 20 yana shugabantar Rasha a matsayin firai minista da shugaban kasa, shugabanci mai cike da rikici da manyan harkokin wasanni.

Bill Clinton yana shugaban Amurka lokacin da tsohon jami'in na KGB ya fara zama shugaban kasar Rasha a ranar 31 ga watan Disamban 1999.

An yi wasu shugabanni uku a Amurka da firai ministoci biyar a Birtani a cikin shekara 20 din.

Za mu kalli shekara 20 ta mulkin Putin a Rasha, kama daga rikice-rikicen duniya zuwa badakala a cikin gida da nasarori a harkar wasanni da kuma hotunan farfaganda.

Putin na gaisawa da Boris Yeltsin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An nada Vladimir Putin a matsayin firai minista a watan Agustan 1999 kafin ya maye gurbin Boris Yeltsin a matsayin shugaban kasar a ranar 31 ga watan Disamba

Tsohon jami'in na KGB ne firai ministan Rasha a lokacin da kasar ta kaddamar da yakin Chechnya na biyu a watan Oktoban 1999, a matsayin martani ga hare-haren bam da aka kai wa rukunin wasu gidaje.

Ana kwatanta farkon shugabancin da rikicin kudancin Chechnya. Dakarun Rasha sun mamaye Grozny babban birnin na Chechnya.

A shekarar 2003, Majalisar Dinkin Duniya ta kwatanta Grozny a matsayin birnin da aka fi lalatawa a duniya a lokacin mamayar.

Putin yana tuka jirgin yaki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mista Putin ya je Chechya a jirgin sama a watan Maris na 2000, 'yan watanni bayan kaddamar da yakin Chechnya na biyu

Masu tayar da kayar baya sunyi shekaru suna kai hare-hare a Rasha, inda a 2004 suka kai harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 330, yawancinsu kananan yara.

Shugaba Putin bai sanar da kawo karshen yakin Chechnya a hukumance ba sai a 2009.

Putin da 'yan majalisar ministocin Rasha sun yi shiru na minti daya domin juyawin mutunen da 'yan tayar da baya suka kashe a wata makaranta

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto, 'Yan majalisar ministocin Rasha sun yi shuru na minti daya domin juyayin mutuwar mutum 330 da 'yan tayar da kayar baya suka kashe a wata makaranta a watan Satumban 2004

A watan Maris na 2000 ne aka tabbatar da Putin a matsayin shugaban Rasha. Watanni kadan bayan nan ne ya dauki hankali kan matsalar hulda da jama'a.

Ma'aikata 118 sun mutu a wani hatsarin jirgi mai tafiya a karkashin ruwa.

Putin na ganawa da dangin wadanda hadarin jirgin Kursk

Asalin hoton, ITAR-TASS/AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Mista Putin yana ganawa da iyalan kwamandan jirgin Kursk, sai dai ya sha suka sosai kan matakin da ya dauka game da hatsarin

Sai da aka shafe kwanaki bayan nutsewar jirgin yakin Kursk mai tafiya a karkashin ruwa kafin Rasha ta sanar da iyalan mamatan, kuma da farko shugaban bai katse hutunsa da yake yi a tekun Black Sea ba.

Putin da tsohon shugaban Amurka George W Bush a Texas, 2001

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Amurka George Bush ya gayyaci Mista Putin ziyarar aiki a 2001. Shugabannin sun je Texas mahaifar Bush a lokacin ziyarar

A shekarun farko na mulkinsa, Vladimir Putin na da kyakkyawar dangantaka da kasashen Yamma duk da cewa yana sukar tsare-tsarensu na harkokin kasahen waje.

Putin da Berlusconi sanye da kayan sanyi sadda da suka je wani gandun namun daji da ke arewacin Moscow a 2003

Asalin hoton, ITAR-TASS/AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Firai ministan Italiya Silvio Berlusconi (a hannun dama) ya ziyarci Rasha a 2003 domin tattauna halin da ake ciki a kasar Iraki
Sarauniya Elizabeth II da Vladimir Putin a cikin keken dawaki a 2003

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarauniyar Ingila ta gayyaci Putin ya kai ziyarar aiki Birtaniya a 2003 - ziyarar farko da shugaban Rasha ya kai tun daga 1874

Rasha ta karbi bakuncin taron kasashen G8 a karon farko a 2006, abin da ke tabbatar da ita a matsayin daya daga cikin kasahen kungiyar kasashen masu karfin tattalin arziki.

Daga hagu zuwa dama: Angela Merkel, Tony Blair, Jacques Chirac, Vladimir Putin da George W Bush

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Angela Merkel da Tony Blair da Jacques Chirac da Vladimir Putin da George Bush sun tsaya a dauke su hoto a taron G8 na St Petersburg

Kundin tsarin mulkin Rasha bai amince Putin ya yi shuganacin kasar sau uku a jere ba a matsayin firai minista, don haka a 2008 ya zama shugaban kasa na tsawon shekara hudu.

A wancan lokaci mutane da dama sun yi ta daukar shugaba Dmitry Medvedev a matsayin yaron Putin da ke rike wa uban gidan nasa mukamin.

Vladimir Putin (na biyu daga hagu) yana kallon wani mutun da aka raunata a lokacin wani fada a kudancin Ossetia, a ziyarar da Putin dai ya kai wani asibiti a Vladikavkaz, hedikwatar arewaacin North Ossetia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mista Putin ya kai ziyara a matsayinsa na firai minista, ga majinyata bayan barkewar yaki a Georgia

Georgia ta tura dakarunta domin kwato yankin kudancin Ossetia da ya balle a 2008, Rasha ta kutsa zuwa cikin Georgia sosai.

Gajeren yakin na watan Agusta gargadi ne ga kasashen Yammacin duniya, amma dabarar Rasha ce ta kutsawa zuwa gabashin Ukraine a 2014, abin da ya kawo tsamin dangantaka tsakanin Putin da kasashen Yamma.

Kwace yankin Crimea da Rasha ta yi daga Ukraine ya sa Amurka da Tarayyar Turai sanya takunkumi da kuma dakatar da Rasha daga kungiyar G8.

Hoton Putin a kan allon talabijin yana sanar da mayar da yankin Crimea karkashin ikon Rasha

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto, Mayar da yankin Crimea karkashin ikon Rasha ya sa Putin ya samu gagarumin goyon baya a zaben jin ra'ayoyin jama'a na 2014
Putin tare da gungun masu babura a Crimea, 2019

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto, Lokacin da Mista Putin ya halarci gangamin masu babura a yankin Crimea a watan Agusta, abin da Ukraine ta kira keta huruminta
Volodymyr Zelensky, Emanuel Macron, Vladimir Putin da kuma Angela Merkel a birnin Paris a watan Disamban 2019

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A watan nan ne aka ci gaba da tattaunawa da Shugaba Volodymyr Zelensky, shekara biyar bayan rikicin na Ukraine, domin kawo karshen rikicin

Shekara hudu bayan fara yakin basasa a Syria, Rasha ta shiga domin goyon bayan abokinta shugaba Bashar al-Assad, wanda gwamnatinsa ke daf da faduwa.

Matakin da Putin ya dauka na tura jiragen yaki da makamai ga Assad ya bude sabon shafi a rikicin na Syria.

Putin tare da Bashar al-Assad a 2017

Asalin hoton, TASS/Getty

Bayanan hoto, Goyon bayan da Putin ke yi wa Bashar al-Assad ya sauya halin da ake ciki a yakin basasar Syria

Bayan nasarar Donald Trump a zaben Amurka na 2016, hukumar binciken kwakwaf ta kasar ta ce Rasha ta yi katsalandan a yakin neman zaben.

Putin na musafaha da shugaban Amurka Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hukumar leken asirin Amurka ta ce Rasha ta yi katsalandan a yakin neman zaben shugaban Amurka na 2016

A 2008 kuma, Birtaniya ta zargi Rasha da kokarin kashe mata tsohon jami'in tsaronta Sergei Skripal a Salisbury ta hanyar ba shi guba.

Theresa May na gaisawa da Vladimir Putin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dangantaka ta yi tsami tsakanin firai ministar Birtaniya ta wancan lokacin Theresa May da Putin bayan bai wa Sergei Skripal guba

A tsawon mulkinsa a matsayin firai ministan Rasha, Putin ya yi kokarin kare kimarsa da ta kasarsa. Hotuna da dama da shugaban ya wallafa a tsawon shekarun sun yi ta nuna shi a matsayin kakkarfa.

Putin rike da bindiga yana farautaba riga a jikinsa

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto, Putin a tube yana dauke da bindiga a iyakar Rasha da Mongolia a 2007
Putin tare da karnukansa Buffy and Yume a 2003

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A 2003 Mista Putin ya fitar da hotunansa a cikin dusar kankara tare da karnukansa Buffy da Yume
Vladimir Putin ya zame a lokacin wasan kwallon gora na kan kankara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Putin ya yi kokarin tallata kwarewarsa a bangaren wasanni. Ya yi ta shiga wasannin Judo da kwallon gora na kankara yana shugaban kasa

Ya kuma yi kokarin bunkasa martabar Rasha a bangaren wasanni, inda kasar ta karbi bakuncin gasar Olympic a 2014 da kuma gasar cin Kofin Duniya na 2018.

An samu nasara a gasar Olympic ta Sochi, amma kuma ana ci gaba da ganin tasirin badakalar amfani da abubuwan kara kuzarin 'yan wasa.

Hukumar yaki da amfani da abubuwan kara kuzari a wasanni ta duniya ta sanya wa Rasha takunkumin shekara hudu a manyan wasanni.

A 2015 wani rahoto ya zargi Rasha da gudanar da shirin amfani da abubuwan kara kuzari a wasanni.

A watan nan da ake ciki, an samu Rasha da laifin jirkita bayanan gwaje-gwajen da aka gudanar a watan Janairu.

Putin na nuni zuwa ga kofin duniya na kwallon kafa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Putin ya taka muhimmiyar rawa don ganin Rasha ta karbi bakuncin gasar cin Kofin Duniya na 2018

Duk da cewa an yi nasara a gasar cin Kofin Duniya ta 2018, badakalar amfani da abubuwan kara kuzari na nufin Rasha ba za ta iya shiga gasar mai zuwa ba a Qatar a shekarar 2022.