Shekara 20 ta Vladimir Putin cikin hotuna 20

Vladimir Putin na shirin bikin cikarsa shekara 20 yana shugabantar Rasha a matsayin firai minista da shugaban kasa, shugabanci mai cike da rikici da manyan harkokin wasanni.

Bill Clinton yana shugaban Amurka lokacin da tsohon jami'in na KGB ya fara zama shugaban kasar Rasha a ranar 31 ga watan Disamban 1999.

An yi wasu shugabanni uku a Amurka da firai ministoci biyar a Birtani a cikin shekara 20 din.

Za mu kalli shekara 20 ta mulkin Putin a Rasha, kama daga rikice-rikicen duniya zuwa badakala a cikin gida da nasarori a harkar wasanni da kuma hotunan farfaganda.

Tsohon jami'in na KGB ne firai ministan Rasha a lokacin da kasar ta kaddamar da yakin Chechnya na biyu a watan Oktoban 1999, a matsayin martani ga hare-haren bam da aka kai wa rukunin wasu gidaje.

Ana kwatanta farkon shugabancin da rikicin kudancin Chechnya. Dakarun Rasha sun mamaye Grozny babban birnin na Chechnya.

A shekarar 2003, Majalisar Dinkin Duniya ta kwatanta Grozny a matsayin birnin da aka fi lalatawa a duniya a lokacin mamayar.

Masu tayar da kayar baya sunyi shekaru suna kai hare-hare a Rasha, inda a 2004 suka kai harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 330, yawancinsu kananan yara.

Shugaba Putin bai sanar da kawo karshen yakin Chechnya a hukumance ba sai a 2009.

A watan Maris na 2000 ne aka tabbatar da Putin a matsayin shugaban Rasha. Watanni kadan bayan nan ne ya dauki hankali kan matsalar hulda da jama'a.

Ma'aikata 118 sun mutu a wani hatsarin jirgi mai tafiya a karkashin ruwa.

Sai da aka shafe kwanaki bayan nutsewar jirgin yakin Kursk mai tafiya a karkashin ruwa kafin Rasha ta sanar da iyalan mamatan, kuma da farko shugaban bai katse hutunsa da yake yi a tekun Black Sea ba.

A shekarun farko na mulkinsa, Vladimir Putin na da kyakkyawar dangantaka da kasashen Yamma duk da cewa yana sukar tsare-tsarensu na harkokin kasahen waje.

Rasha ta karbi bakuncin taron kasashen G8 a karon farko a 2006, abin da ke tabbatar da ita a matsayin daya daga cikin kasahen kungiyar kasashen masu karfin tattalin arziki.

Kundin tsarin mulkin Rasha bai amince Putin ya yi shuganacin kasar sau uku a jere ba a matsayin firai minista, don haka a 2008 ya zama shugaban kasa na tsawon shekara hudu.

A wancan lokaci mutane da dama sun yi ta daukar shugaba Dmitry Medvedev a matsayin yaron Putin da ke rike wa uban gidan nasa mukamin.

Georgia ta tura dakarunta domin kwato yankin kudancin Ossetia da ya balle a 2008, Rasha ta kutsa zuwa cikin Georgia sosai.

Gajeren yakin na watan Agusta gargadi ne ga kasashen Yammacin duniya, amma dabarar Rasha ce ta kutsawa zuwa gabashin Ukraine a 2014, abin da ya kawo tsamin dangantaka tsakanin Putin da kasashen Yamma.

Kwace yankin Crimea da Rasha ta yi daga Ukraine ya sa Amurka da Tarayyar Turai sanya takunkumi da kuma dakatar da Rasha daga kungiyar G8.

Shekara hudu bayan fara yakin basasa a Syria, Rasha ta shiga domin goyon bayan abokinta shugaba Bashar al-Assad, wanda gwamnatinsa ke daf da faduwa.

Matakin da Putin ya dauka na tura jiragen yaki da makamai ga Assad ya bude sabon shafi a rikicin na Syria.

Bayan nasarar Donald Trump a zaben Amurka na 2016, hukumar binciken kwakwaf ta kasar ta ce Rasha ta yi katsalandan a yakin neman zaben.

A 2008 kuma, Birtaniya ta zargi Rasha da kokarin kashe mata tsohon jami'in tsaronta Sergei Skripal a Salisbury ta hanyar ba shi guba.

A tsawon mulkinsa a matsayin firai ministan Rasha, Putin ya yi kokarin kare kimarsa da ta kasarsa. Hotuna da dama da shugaban ya wallafa a tsawon shekarun sun yi ta nuna shi a matsayin kakkarfa.

Ya kuma yi kokarin bunkasa martabar Rasha a bangaren wasanni, inda kasar ta karbi bakuncin gasar Olympic a 2014 da kuma gasar cin Kofin Duniya na 2018.

An samu nasara a gasar Olympic ta Sochi, amma kuma ana ci gaba da ganin tasirin badakalar amfani da abubuwan kara kuzarin 'yan wasa.

Hukumar yaki da amfani da abubuwan kara kuzari a wasanni ta duniya ta sanya wa Rasha takunkumin shekara hudu a manyan wasanni.

A 2015 wani rahoto ya zargi Rasha da gudanar da shirin amfani da abubuwan kara kuzari a wasanni.

A watan nan da ake ciki, an samu Rasha da laifin jirkita bayanan gwaje-gwajen da aka gudanar a watan Janairu.

Duk da cewa an yi nasara a gasar cin Kofin Duniya ta 2018, badakalar amfani da abubuwan kara kuzari na nufin Rasha ba za ta iya shiga gasar mai zuwa ba a Qatar a shekarar 2022.