An tsare matar mataimakin shugaban Zimbabwe saboda rashawa

Matar mataimakin shugaban kasar Zimbabwe Constantino Chiwenga, na tsare a hannun jami'an tsaro saboda zarginta ta ta'ammuli da haramtattun kudaden kasashe waje.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawar kasar ta ce an tsare Marry Mubaiwa ne a yammacin Asabar. Gobe Litinin ne ake sa ran gurfanar da ita a gaban kotu.

Tuhumar da ake wa Marry ta hada da batun sayen motocin alfarma guda biyu da ta yi a Afirka ta Kudu.

Rahotanni na cewa Marry na bin wata kazamar hanyar neman rabuwa da mijinta, wanda aka jima ana ganinsa a matsayin babbar barazana ga shugaba Emmerson Mnangagwa a siyasance.

Shugaba Mnangagwa na fuskantar karin matsin lamba a kan matsalar tattalin arzikin kasar, kuma ya yi alkawarin magance matsalar cin hanci da rashawa.