Kotu ta daure tsohon shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir kan rashawa

Kotu a Sudan ta daure tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir saboda laifin karbar rashawa.

An daure tsohon shugaban har na tsawon shekara biyu a gidan gyara hali, karbar dala miliyan 25 tsaba daga Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya Mohammed bin Salman.

Kotun ta umurci kwace kudaden daga tsohon shugaban da sojoji suka hambarar da gwamnatinsa a watan Afrilu. Ta kuma ba da umurnin mayar da al-Bashir zuwa inda ake tsare da shi domin cigaba da bincikar sa kan zargin juyin mulkin da ya kawo gwamnatinsa a 1989.

Alkalin ya bayyana cewa a bisa tsarin dokar kasar ba za a iya kai al-Bashir gidan kaso ba saboda ya wuce shekara 70.

Omar al-Bashir na kuma fuskantar shari'a kan juyin mulkin da ya kawo gwamnatinsa a shekarar 1989 da zargin aikata kisan kiyashi da kuma kashe masu zanga-zanga kafin a hambarar da shi a watan Afrilu.

A lokacin da ake gabatar da hukuncin, magoya bayan al-Bashir na ta kuwwar cewa "siyasa ce", kafin a kora su.

Sai suka koma gefe inda suke ta yin Kabbara.

Har yanzu dai ba a san cewa ko a za tuhumi al-Bashir kan cin zarafin bil adama da ya auku a lokacin mulkinsa ba da kuma zargin aikata laifukan yaki a Darfur.

Me 'yan adawa suka ce?

Yan adawa a Sudan na zargin sassauci a hukuncin daurin shekara biyu da kotu ta yanke wa tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir.

Sai dai alkalin ya ce kotun ba ta da hurumin daure al-Bashir wanda ya haura shekara 70 a gidan yari, a don haka sai dai a tsare tsoho shugaban a gidan gyara halinka.

Jaridar Al-Taghyeer ta masu adawa a Sudan ta ce hukuncin kotu ya yi sassauci ga al-Bahir wanda ya mulki kasar na tsawon shekara 30.