Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kama dan kunar bakin waken IS a Morocco
Jami'an tsaro sun tsare wani da ake zargin dan kunigiyar IS ne yana kokarin kai harin kunar bakin wake a birnin Meknes na kasar
Ma'aikatar bincikin manya laifuka ta Morocco BCIJ ta ce mutumin na dauke da na'urori da wasu takardun hada abubuwa masu fashewa a sadda aka tsare shi.
A baya-bayan nan gwamnatin kasar ta sanar da tarwatsa wasu gungun 'yan ta'adda.
A farkon watan Disamban nan da muke ciki ne jami'an tsaro kasar suka kama wasu 'yan ta'adda mutum uku a yankin Nador kasr Morocco.
Hadin gwiwan da jami'an suka yi da 'yan sanda a kasar Spain ya yi sanadiyar kama wani dan ta'addan da ke hada baki da wadanda aka kama a Moroccon da can Spain din.
Wasu 'yan ta'addan mutum uku kuma an kama su ne Rabat da Marrakech a tsakiyar watan Nuwamba a Morocco.