Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An daure 'yar jaridar Morocco saboda zubar da ciki
An yanke wa wata 'yar jaridar Morocco hukuncin daurin shekara daya a gidan yari saboda samun ta da laifin zina da zubar da ciki, a wani mataki da masu fafutuka suka ce na musgunawa 'yan jaridar da ke ba da labaran da ba sa yi wa hukumomi dadi ne.
An kama Hajar Raissouni da saurayinta lokacin da suka je asibitin mata da ke Rabat, babban birnin kasar a watan Agusta.
'Yar jaridar mai shekara 28 ta musanta tuhumar da aka yi mata, tana mai cewa ta je asibitin ne domin neman magani kan zubar da jinin da take yi.
Ms Raissouni tana aiki a gidan jarida mai zaman kansa wanda ke buga labaran da ba sa yi wa hukumomi dadi.
Tana aiki a jaridar Akhbar Al-Yaoum wacce ake wallafawa kullum, kuma ta ce hukuncin da aka yanke mata na da alaka da "siyasa", tana mai cewa 'yan sanda sun taba yi mata tambayoyi kan iyalinta da kuma rubuce-rubucenta.
Ms Raissouni ta isa kotun da ke Rabat sanye da bakin gyalen da ya rufe fuskarta. Ita da saurayinta, dan kasar Sudan, sun musanta zargin zubar da ciki.
"Mun yi matukar kaduwa da jin wannan hukunci," in ji lauyanta, Abdelmoula El Marouri, a tattaunawarsa da kamfanin dillancin labaran Reuters, yana mai cewa ya kamata a sallame ta da an yi la'akari da takardun asibiti da shaidun shari'ar da suka gabatar.
Ya kara da cewa za su daukaka kara kan hukuncin.
Mai shigar da kara ya ce kamun da aka yi wa 'yar jaridar ba shi da alaka da aikinta na jarida, yana mai cewa hukumomi sun sanya ido sosai kan asibitin saboda zargin zubar da ciki ba bisa ka'ida ba.
Kotu ta yanke wa saurayinta hukuncin zaman gidan yari na shekara daya inda kuma ta yanke hukuncin daurin shekara biyu kan likitanta.
Kazalika an samu mataimakin likitan da nas din da suka yi aiki tare da laifi ko da yake an yanke musu hukuncin je-ka-gyara-halinka.
Ahmed Benchemsi, shugaban kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch a yankin, ya bayyana hukuncin a matsayin wani mataki na rufe bakin 'yan jarida da hana fadin albarkacin baki.