Zanga-zangar Lebanon ta kara tsananta sosai

Zanga-zangar da aka yi a tsakiyar birnin Beirut ta kai cikin dare

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Zanga-zangar da aka yi a tsakiyar birnin Beirut ta kai tsakiyar dare

Wata arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga ta jikkata mutane da dama a Beirut babban birnin Lebanon.

Akalla mutum 54 jikkata, cikinsu har da jami'an 'yan sanda 20. 'Yan sanda sun yi ta harba hayaki mai sa hawaye da harsashen roba, yayin da masu zanga-zangar suka yi ta jifan su da duwatsu.

Zanga-zangar kin amincewa da rashin iya gudanar da tattalin arziki a Lebanon ce ta yi sanadiyyar saukar firai minista Saad al-Hariri.

Amma har yanzu an kasa cimma matsaya a kan kafa sabuwar gwamnati a kasar.

Rikici ya kaure ne bayan wasu masu zanga-zangar zaman dirshen sun yi kokarin kutsawa cikin wani dandalin taro da ke kusa da zauren majalisar dokokin kasar.

Ba'a taba samun babbar zanga-zanga irin wannan ba a cikin shekara goma a Lebanon. Ita ce zanga-zangar da ta taba game baganrorin kasar tun bayan yakin basasar kasar ta 1975-1990.

Hakan ya faru ne bayan gungun wasu masu zanga-zanga da suka rufe fuskokinsu suka kai wa masu zaman dirshen din farmaki.

Rikicin na ranar Asabar na daga cikin mafiya muni da aka samu tun da aka fara gudanar da zanga-zangar lumana a Lebanon.

"Zanga-zangar lumana ce. Kowa na waka, muna cewa mu al'umma daya ce, kuma muna cikin lumana.

Ana cikin haka sai ga wasu daga cikin matasa suka ture daya daga cikin shingayen da suka raba tsakaninmu," inji Mona Fawaz, daya daga cikin masu zanga-zangar.

Sai muka ga wani cincirindon 'yan sanda suka fito suka watsa mu, suna kora mu sannan suka fara harba mana hayaki mai sa hawaye. Babu dalilin yin amfanin da karfin da ya wuce misali."

Akalla mutane 54 ne suka samu rauni, inji ma'aikatar tsaro ta farin kaya ta Lebanon

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Akalla mutane 54 ne suka samu rauni, inji ma'aikatar tsaro ta farin kaya ta Lebanon

Rahotanni daga Reuters na cewa an girke 'yan sandan kwantar da tarzoma da wasu jami'an tsaro domin kora masu zanga-zangar, inda suke duka tare da tsare wasu daga cikin masu zanga-zangar.

An yi ta arangama tsakanin bangarorin har cikin dare inda masu zanga-zangar suka tsallake shingen da ya tare hanyar zuwa majalisar da wasu gine-ginen gwamati.

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun kama wani mai zanga-zangar kin jinin gwamnati a lokacin arangamar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, 'Yan sandan kwantar da tarzoma sun kama wani mai zanga-zangar kin jinin gwamnati a lokacin arangamar

Mansu zanga-zangar sun fusata ne da gazawar shugabanni wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, da kuma hauhawar farashi da karuwar rashin aiki da rashawa da kuma lalacewa ababen rayuwa.

Suna bukatar a kawo karshen rashawa a cikin gwamanti da yi wa tsarin siyaryar kasar garambawul sannan a kafa majalisar kasar marar alaka da akida ko bangaranci.

A gobe Litinin ne ake sa ran shugaba Michel Aoun da bangarorin majalisar kasar za su tattauna batun ayyana sunan sabon firai ministan kasar.