Matsalar tsaro: Gwamnatin Zamfara 'ba da gaske take ba'

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle

Asalin hoton, @Bellomatawalle1

Kwamitin da gwamnatin Zamfara a arewacin Najeriya ta kafa domin gano tushen matsalar tsaron jihar ya ce gwamnatin ta gaza wajen aiwatar da shawarwarin da ya bayar.

Kwamitin na mutum tara karkashin jagorancin tsohon sufeto janar na 'yan sandan Najeriya MD Abubakar, ya ce sama da wata biyu kenan da gabatar da rahoton ga gwamnan Jihar Bello Matawalle amma ba abin da aka yi.

Daga cikin manyan shawarwarin da kwamitin ya bayar sun hada da tube wasu manyan sarakunan gargajiya guda biyar da uwayen kasa 33 da kuma Hakimai da dama wadanda kwamitin ya zarga da hannu a kashe-kashen jihar da satar mutane domin kudin fansa.

Akwai kuma jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda da kwamitin ya zarga tare da bayar da shawarar a hukunta su.

Dakta Sani Abdulahi Shinkafi daya daga cikin mambobin kwamitin, ya shaida wa BBC cewa jan kafar ya nuna cewa gwamnatin jihar ta Zamfara ba da gaske take ba.

"An kafa kwamiti an kashe kudin mutane kuma an kasa aiwatar da rahoton da aka bayar," in ji shi.

Sai dai kuma gwamnatin Zamfara ta ce tana nazari ne kan rahoton, kuma idan ta kammala za ta aiwatar da dukkanin shawarwarin da kwamitin ya batar.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Zailani Baffa ya shaida wa BBC cewa ba za a yi gaggawar aiwatar da rahoton ba tare da nazari ba.

A cewar Zailani, gwamnatin Matawalle tana nazarin rahoton kuma za ta aiwatar ba tare shiga hakkin kowa ba, sai dai bai fadi lokacin da za ta kammala nazarin rahoton ba.

Tun karbar rahoton a watan Oktoba, gwamnan jihar ya yi alkawalin cewa a shirye gwamnatinsa take ta aiwatar da shawarwarin kwamitin da ta kafa wanda ya gudanar da bincike game da matsalar 'yan bindiga da satar mutane da suka addabi jihar.

Dakta Shinkafi daya daga cikin mamban kwamitin na MD Abubakar ya ce shawarwari 296 suka bayar kuma guda uku kawai ya ce gwamnatin ta aiwatar wato cire Sarkin Maru.

Da kuma kafa tubali da gina ruga ta fulani a Maradun.

Ya ce rashin aiwatar da manyan shawarwarin da kwamitin ya bayar ya nuna ba da gaske gwamnatin take yi ba.

A cewarsa bincikensu ya gano cewa mutum 6319 aka kashe a Zamfara, sannan an bar marayu 25050 da mata 6536 da aka kashe mazajensu.

Sannan ya ce an karbi kudin fansa fiye da naira da biliyan biyu da kuma sace dambobi kusan 350,000.

Haka kuma kashe-kashen Zamfara ya tursasawa mutum 276,000 yin gudun hijira.

An shafe shekaru Jihar Zamfara na fama da har-haren 'yan bindiga masu fashin shanu da satar mutane.