Za mu cire sarakuna a Zamfara - Matawalle

Asalin hoton, @Bellomatawalle1
Gwamnatin Zamfara ta ce a shirye take ta aiwatar da shawarwarin kwamitin da ta kafa wanda ya gudanar da bincike game da matsalar 'yan bindiga da satar mutane da suka addabi jihar.
Kwamitin dai ya bayar da shawarwari 132 kuma daga cikinsu akwai shawarar tube wasu sarakunan gargajiya 5 da hakimai 33, wadanda kwamitin ya zarga da hannu dumu-dumu cikin al'amarin matsalar tsaron Zamfara.
Akwai kuma jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda da kwamitin ya zarga tare da bayar da shawarar a hukunta su.
Yusuf Idris Gusau daraktan watsa labarai na gwamnan jihar, Bello Matawalle, ya shaida wa BBC cewa gwamnan ya karbi rahoton kuma ya yi alkawalin aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar.
Sai dai ya ce gwamnati za ta fara ne da shawarwarin da ke bukatar daukar matakin gaggawa.
Sau da dama a Najeriya ana ganin yadda ake watsi da shawarwari na irin wadannan kwamatoci da akan kafa a jihohi da ma tarayya.
Kwamitin binciken ya ce ya samu hujjoji ne daga mutum 3,700 da suka bayyana gabansa sakamakon tarin takardun korafin da aka gabatar musu.
Sanata Dansadau mamba a kwamitin ya shaida wa BBC cewa sun karbi bahasi ne daga 'Yan ta'addan da suka tuba da Fulanin da aka sace shanunsu wadanda suka yi bayani dalla-dalla kan wadanda ke da hannu a kashe-kashen da kwamitin yake zargi.
An shafe shekaru takwas Jihar Zamfara na fama da har-haren 'yan bindiga masu fashin shanu da satar mutane.
A ci gaba da tabbatar da tsaro a Zamfara rundunar sojin Najeriya ta Operation Hadarin Daji ta ce ta yi nasarar murkushe harin da 'yan bindiga suka kai wa jami'anta a wani kauye da ke karamar Hukumar Anka.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Sai dai ta ce sojojinta hudu ne suka mutu yayin da suka kashe 'yan bindiga 19 a harin Sunke.
Ta kuma ce ta kashe 'yan bindiga 39 a Bawa Daji ciki har da wani kwamandansu da ake kira Emir a samamen da ta kai sansanonin 'yan bindigar guda uku inda ta kwace makamai da bindigogi kirar AK 47 da shanu.











