Zamfara: An rufe makaranta sakamakon wulakanta Al-Kur'ani

Asalin hoton, @Hudu_Matawalle
Gwamnan jihar Zamfara Dakta Mohammed Bello Matawalle ya bayar da umarnin rufe wata makarantar firamare a jihar sakamakon yadda ake wulakanta Al-Kur'ani.
Hakan ya faru ne bayan saka Al-Kur'ani a cikin masai na wata makarantar firamare da ke jihar.
A wata sanarwa da daraktan watsa labaran gwamnatin jihar ya fitar, ta bayyana cewa gwamnan ya bada umarnin rufe ''Shattima Model Primary School,'' da kuma dakatar da malamanta daga aiki.
Hakazalika ya kuma umarci hukumar kula da ilimi a matakin farko ta jihar da kara daukar masu gadi uku-uku domin kai su makarantun firamare na Zamfara baki daya domin tsaurara tsaro.
Gwamnan ya kuma ba jami'an tsaron jihar da kuma hukumomin da ke aiwatar da harkokin Shari'a umarnin kafa kwamiti domin gudanar da bincike kan yadda ake wulakanta Al-Kur'ani mai girma a jihar.
Gwamnan ya sha alwashin daukar tsatsauran mataki ga duk wanda aka samu da hannu wajen wulakanta Al-Kur'ani a jihar.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya yi kira ga manyan malamai a jihar da kuma Najeriya baki daya da su ja hankalin jama'a ta hanyar wa'azi kan aiwatar da irin wadannan munanan dabi'u.
Tun a baya an sha samun irin wannan matsalar a jihar ta Zamfara ta jefa Al-Kur'ani cikin juji ko masai.











