Za a fara koyar da Fulatanci a makarantun Zamfara

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce za ta gabatar da harshen Fulatanci a jadawalin makarantun jihar.
Gwamnatin ta sanar da wannan matakin ne a lokacin da take shirin fara gina rugage a jihar a wannan makon.
Gwamna Bello Matawalle ya bayyana kaddamar da harshen ne a Gusau, babban birnin jihar a lokacin da ya karbi tsarin gina rugagen.
Matawalle ya ce "Tun da mun yi alkawarin bude makarantun firamare da sakandire a sabbin rugagen da zamu gina, za mu tabbatar an yi amfani da harsunanmu na gargajiya don ka da su bace."
Gwamnan ya bayyana cewa wannan zai habaka harsunan gargajiya musamman ga yara masu tasowa.
Tuni Gwamna Matawalle ya umarci ma'aikatar ilimin jihar ta gaggauta fara aiki kan sabon tsarin a makarantu.
Kwakin baya ne dai gwamnatin Najeriya ta bayyana shirinta na gina rugage a jihohin kasar don tsugunar da makiyaya a waje guda.
Matakin ya jawo ce-ce-ku-ce a fadin kasar musamman daga 'yan bangaren kudanci, inda suka soki samar da rugagen ga Fulani makiyaya.
Gwamnatin jihohin kudu ma ba a bar su a baya ba, inda tuni gwamnonin yankin kudu maso gabashin Najeriya suka kekashe kasa cewa ba za su shiga wannan shiri ba.
Su kansu al'ummar Fulani sun ce su fa sun fi son a bar su su ci gaba da yawo da shanunsu maimakon tsugunar da su da gwamnati ke shirin yi.
Ardo Sa'idu Baso shi ne sarkin Fulanin kudu maso gabas a Najeriya, ya ce ai in so samu ne a ce wata uku ko hudu shanunka su sauya wurin zama.
Ya ce: "Mu a bar mu haka muna yawace-yawace da shanunmu ya fi mana a kan a tsugunar da mu a wuri daya. Inda shanu suka yi bazara ba nan suke shekara ba.
"Ya kamata a ce wata uku ko hudu shanu su sauya wurin zama, mu mun fi jin dadin hakan."
Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin da suka rungumi tsarin, kuma ta farko a jihohi da ta fara aikin gina rugagen.











