Abin da sabuwar dokar masarautun Kano ta kunsa

    • Marubuci, Daga Imam Saleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu a kan dokar samar da karin masarautu hudu a jihar a karo na biyu, da suka hada da masarautar Bichi, da Rano, da Karaye, da kuma Gaya.

Majalisar dokokin jihar ce ta mika wa gwamnan dokar bayan tsallake karatu na uku sannan ta zama doka.

Dama dai majalisar a baya ta taba amincewa da kudurin, sai dai daga bisani wata babbar kotu a jihar ta rushe ta bisa hujjar rashin cika ka'ida kafin yinta, abin da ya sa gwamnan ya sake gabatar wa majalisar kudurin a karo na biyu.

Matakin majalisar na amincewa da kudurin a wannan karon ya zo ne duk da umarnin wata babbar kotun jihar na cewa kada wanda ya dauki wani mataki kan batun har sai ta saurari karar da masu zabar sarkin Kano suka shigar gabanta, suna kalubalantar kirkiro sabbin masarautu a jihar.

Tanadin da dokar ta yi

Da farko dai dokar ta yi tanadi 51, in ji shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano Labaran Abdul Madari, a yayin tattaunawarsa da BBC.

"40 daga cikinsu dama ana amfani da su tun lokacin da ake gudanar da tsarin masarauta daya a jihar," a cewarsa.

Ga wasu muhimmai daga cikin su.

  • Gwamna ne zai zabi shugaban majalisar sarakuna da za a kafa nan gaba
  • Gwamna ne zai nada masu zabar sarki a duk lokacin da bukatar hakan ta taso
  • Duk sarkin da gwamna ya zaba don shugabantar majalisar sarakuna, zai jagoran ce ta ne tsawon shekaru biyu
  • Duk sarkin da yaki halartar tarukan majalisar sarakunan har sau uku ba tare da kwakkwaran dalili ba, ya kori kansa daga sarauta.

An yi ta yada cewa wata sadara a dokar ta yi tanadin cewa ''Kowanne sarki a jihar ba shi da damar bai wa gwamna shawara har sai gwamnan ya nemi hakan daga gare shi,'' da kuma cewa ''Gwamna na da damar ragewa kowanne sarki daraja a duk lokacin da yaso.''

Sai dai shugaban masu rinjaye na majalisar Labaran Abdul Madai ya ce wadannan maganganun biyu ba gaskiya ba ne.

Martanin masana shari'a

Tun gabanin majalisar Kano ta amince da wannan kudurin doka, masana shari'a da dama suka fara bayyana ra'ayoyinsu.

Da damansu sun ja hankalin majalisar cewa za ta kara yin abin da ya saba doka kasancewar kotun ta ce a rushe sarakunan, amma ba a rushe su ba. Sannan akwai wata shari'ar dangane da batun a gaban wata kotun.

Barista Umar Danbaito, wani lauya ne mai zaman kansa a jihar Kano, ya ce majalisar ta gina wannan doka ne "a kan tubalin toka," domin tun farko hukunci biyu kotun da ta rushe masarautun ta yi.

"Na farko shi ne ta rushe dokar da ta samar da sarakunan, bi ma'ana ta rushe sarakunan kenan, sai kuma hukunci na biyu da ya umarci majalisar ta dakatar da amincewa da kudurin har illa masha'allahu.

"Don haka kotun da ta yanke hukuncin za ta iya garkame 'yan majalisar da suka amince da kudurin tun da sun saba da umarninta, kazalika za ta iya sake rushe masarautun a nan gaba.

''Duk mahalukin da yake ganin wuyansa ya isa yanka, ta hanyar take umarnin kotu, ba shakka kotu za ta iya angiza shi zuwa gidan kaso, zabi daya kawai yake da shi, ko ya daukaka kara, ko ya amince da hukuncin ko da kuwa ba dai-dai bane," in ji Barista Danbaito.

Kotu ta dakatar da Ganduje sanya wa dokar hannu

Shi kansa gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, akwai hukuncin da alkalin kotun daukaka kara a Kano A T Badamasi ya yanke a ranar 23 ga watan Mayu, da ya hana shi sake bijiro da wannan doka ko kuma tabbatar da ita, ko ma taba masu zabar sarki a masarautar Kano, bayan wata kara da suka shigar suna kalubalantar matakin gwamnan na neman sake kafa wasu masarautu ba tare da ya tuntube su ba.

Wasu masana shari'ar na ganin cewa a yanzu gwamnan yayi watsi da wancan hukunci, ya kuma tabbatar da sarakunan bayan rushe su a baya da kotu tayi.

Me gwamnatin Kano ke cewa?

Mallam Muhammadu Garba, shi ne kwamishinan yada labarai na gwamnatin Kano, ya shaida wa BBC cewa, su a wajen su, babu wani hukunci da alkali yayi na cewa kada 'yan majalisa su tattauna wannan batu, sannan babu wani hukunci da ya hana gwamna tabbatar da dokar ko kuma sanya mata hannu.

''Ba yadda za a yi mu ki bin umrnin kotu, inda ba za mu bi umarnin kotu ba, ai lokacin da kotu ta yanke hukuncin farko, sai mu ce bamu yarda ba, ko mu daukaka kara, amma saboda tunani na gwamnati, aka ga cewa gyara ake so a yi, sai mai girma gwamna ya ce bari mu sake bin ka'ida kamar yadda aka bukata''

Yadda abin ya samo asali

A watan Mayun bana ne gwamnatin Kano ta kirkiri sababbin masarautu hudu a Kano, abin da wasu suke ganin an yi ne domin kassara karfi da tasirin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Gwamnati ta ce an kirkiro sababbin masarautun ne domin tabbatar da ci gaba, to amma wasu majiyoyi na kusa da gwamnati sun ce tana son daukar fansa ne kan rashin goyon bayan da ake zargin Sarki Sanusi bai ba wa Ganduje ba a yayin zaben shekarar 2019, wanda Gandujen ya nemi takara a karo na biyu.

Hukumar karbar korafe-korafen jama'a ta Kano, ta taba cewa Sarki Sanusi ya yi bushasha da kudin masarauta inda kuma ta nemi da a dakatar da shi, sai dai daga baya ta janye bukatarta.

A baya, kungiyar gwamnonin Najeriya da Alhaji Aliku Dangote sun shiga tsakani har ma aka sasanta Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi, sai dai hakan bai hana gwamnatin Kano aiwatar da manufarta ta samar da sabbin masarautun ba.

Masu nada sarki a masarautar Kano

Madakin Kano, Hakimin Dawakin tofa, Yusuf Nabahani.

Makaman Kano, Hakimin Wudil, Abdullahi Sarki Ibrahim

Sarkin Dawaki Mai Tuta, Hakimin Gabasawa, Bello Abubakar

Sarkin Ban Kano, Hakimin Dambatta, Mukhtar Adnan.