Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sabbin Sarakunan Kano: Ko Ganduje zai bi umarnin kotu?
Kwamishinan shari'ah na jihar Kano, Barista Ibrahim Mukhtari ya fada wa BBC cewa har zuwa daren ranar Juma'a, bai karbi wani umarni daga kotu (game da batun nada sabbin sarakuna da kirkirar karin masarautu na gwamnatin Kano) ba.
Babbar kotun jihar Kano ce ta ba da umarnin cewa gwamnati da majalisar dokokin jihar su dakatar da duk wani mataki na kirkirar sabbin masarautu a jihar ta Kano har sai ta saurari karar da wasu 'yan majalisa suka shigar gabanta suna kalubalantar matakin yin dokar.
"Ban san da kara ba, kawai dai yadda kuke ji a gari, (ni ma) haka nake ji a gari." Barista Ibrahim Mukhtari ya ce: "Ni ban ga oda ta kotu ba kowacce iri."
Ya kara da cewa don haka ba za su ce komai a kai ba, har sai sun ga takardar kotu.
Za dai a zuba ido a gani ko gwamnatin jihar Kano za ta dakatar da nadin sarakunan a ranar Asabar kamar yadda ta tsara bisa umarnin kotu, ko kuma za ta yi biris da umarnin ta ci gaba da shagulgulan bai wa sabbin sarakunan hudu sandunan girma.
Sarakunan dai sun hadar da Alhaji Aminu Ado Bayero, zai jagoranci masarautar Bichi, da Dr. Ibrahim Abubakar a matsayin sarkin Karaye sai Tafida Abubakar Ila sarkin Rano da kuma Alhaji Ibrahim Abdulkadir a matsayin sarkin Gaya.
'Yan majalisar bangaren jam'iyyar PDP mai adawa wadanda marasa rinjaye ne suka shigar da karar bisa jagorancin shugabansu Rabiu Sale Gwarzo.
Da ma dai tun lokacin da majalisar ta fara yin gyara kan dokar masarautun, marasa rinjayen suka kauracewa zaman majalisar domin nuna rashin goyon baya ga yunkurin gyaran dokar masarautar Kano.
Lauyan masu kara Barrista Maliki Kuliya Umar ya ce takardar da suka mika gaban kotun ta kunshi bukatar hana 'yan majalisa da gwamnati daukar wani mataki na kirkirar sabbin masarautun, da nada su, da ba su sandar girma.