An kama Sarkin Mayu na bogi mai hada mutane fada a Kano

Ku latsa lasifikar da ke sama don sauraron hirar BBC da Muhuyi Magaji da Khalifa Shehu Dokaji a kan Sarkin Mayun boge

Hukumar karbar korafe-korafe ta jihar Kano a arewacin Najeriya, ta kama wani mutum mai da'awar shi Sarkin Mayu ne tare kuma da damfarar mutane kauyen Albasu.

Shugaban hukumar karbar korafi Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya shaida wa BBC cewar 'Sarkin Mayun' kan bukaci kudi daga hannun wanda ake zargi da kama mara lafiya da maita, a matsayin tara.

Muhuyi Magaji ya ce binciken da suka gudanar ya nuna musu cewar mutumin na amfani da wata ciyawa da yake amfani da ita wajen.