Ko ya dace ma'aikata su rika barci a wurin aiki?

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Amurka ta ce barci ba shi da matsuguni a wuraren aiki, amma kwararru a fannin barci sun ce ya kamata gwamnatin ta sake nazari kan hakan.
Gwamnatin ta yanke shawarar daukar kwakkwaran mataki kan yin barci a wurin aiki.
Duk da ma'aikatan gwamnati sun dade suna sheka barcinsu a wajen aiki, ba a taba yunkurin haramtawa ba sai a wannan lokacin, in ji Jonathan Berr, kwararre a fannin barci.
"An haramtawa mutane barci a gine-ginen gwamnati, sai dai idan hukumomi sun bayar da izinin hakan," kamar yadda sanarwar da gwamnati ta fitar a farkon watan nan ta bayyana.
Kawo yanzu ba a san abin da ya janyo hankalin gwamnati ta dauki matakin ba, kuma sun ki yarda su ce uffan kan hakan duk da sukar da haramcin yake sha.
A shekarar 2018 ofishin babban editan jihar California ya fitar da wani rahoto kan sashen ma'aikata na kamfanonin mota da suke barci na tsawon sa'a uku a kowacce rana a wurin aiki.
Rahoton ya ce barcin da ma'aikatan ke yi ya na janyo asarar dala 40,000 cikin shekara hudu.
Wata ma'aikaciya mai yawan barci na takurawa abokan aikinta, ta yadda suke taimaka wa da yi mata aiki idan ta yi barci.
Shugaban wurin ya damu matuka da yawan barcinta, inda ya fara tunanin ko tana fama da wata rashin lafiya da ke sanyata bacci.

Asalin hoton, Getty Images
Batun haramta wa ma'aikata barci a wurin aiki zai tayar wa da wasu hankali, sai dai ana ta samun musayar ra'ayi kan hakan.
Tsohon shugaban cibiyar kula da magungunan da suke sanya barci, kuma darakta a asibitin mata na Boston Dr Lawrence Epstein ya ce kusan Amurkawa miliyan 70 na fama da matsalar barci.
Wani sabon bincike da Jami'ar Ball ta Indiya ta gudanar, da ya mayar da hankali kan tsawon lokacin da mutane 150,000 ke dauka suna barci, ya gano kashi 35 cikin 100 na mutanen na samun barcin sa'a bakwai ne da dare a shekarar 2018, amma a shekarar 2010 kashi 30 cikin 100 ne ke samun barcin.
Yawancin wadanda aka yi bincike a kansu 'yan sanda ne da jami'an lafiya wadanda suka ce ba sa samun isasshen barci.
Epstein ya shaida wa BBC cewa ''Wasu kamfanonin sun fara gano ma'aikata na samun matsalar rashin barci, don haka sun fara daukar matakai. Sai dai ba na jin gwamnatinmu ba lallai ta dauki mataki ba gaskiya.''
Lamari ne da ya kamata a sake nazari akai, da samun mafita, saboda matsala biyu ce a nan, haramta barcin na nufin barazana ga lafiya, barin yin sa kuma zai shafi tattalin arziki.
Rashin isasshen barci babbar barazana ce ga lafiyar dan adam, cikin cututtukan da rashin barci ke haifarwa akwai sa matsananciyar kiba, da ciwon suga, da zuciya, da shanyewar barin jiki, da kuma shafar kwakwalwa.
Binciken da aka yi a shekarar 2016 da Rand Corporation ya mayar da hankali kan koma bayan da tattalin arikin Amurka ke fuskanta sakamakon barcin da ma'aikata ke yi a wuraren aiki
Amma ga kwararru kamar Epstein, yana goyon bayan a bar ma'aikata su yi barcinsu.
Mutanen da aka hana su barci a wurin aiki ba sa gudanar da aikin yadda ya dace, suna kuma cikin hadarin samun matsala a wurin aikin da a karshen kamfanin zai iya asarar makudan kudade saboda wata sabuwar matsalar da ta kunno kai.
Wasu kasashen ba sa daukar mataki kan ma'aika masu bacci.
Misali kamfanoni a kasar Japan suna sanya wata na'ura da ke dauke minsharin mai barci da nufin karfafa wa ma'aikata gwiwa su dan runtsa idan bukatar hakan ta taso a wurin aiki, amma kar ya wuce kima.
Wasu kamfanoni irin na yin askirim na Ben & Jerry, sun tanadi daki na musamman da za su dinga yin barci lokaci zuwa lokaci.
Dakunan ba dai masu kayatarwa ba ne, amma dai suna kawar da lalurar barci tun da akwai dan karamin gado, da matashin kai da karamin bargo.

Asalin hoton, BIM
Ana umartar masu yin barcin su fara cire takalmansu, kuma suna da dama yin minshari na minti 20. Amma duk ma'aikacin da ba zai iya barcin da bai gaza minti 20 ba, sai dai a kora shi gida.
Duk da wannan dama, tsangwamar da ake nuna wa masu bacci a wurin aiki na karuwa, kamar yadda mai magana da yawun kamfanin askirim Ben & Jerry, Laura Peterson ta shaida wa BBC.
Ta ce kamfanin sun daina sanya alamar wani na bacci a dakin da aka ware, bayan da aka fara kiran wani ma'aikaci da suna"Donald Duck", saboda minshari.
"Ni da kaina ina yin barci a wurin aiki, ina sanya kararrawa a wayata don kar barci ya zarme min. Dan hutu ne mai dadi da sanya zuciya da gangar jiki hutawa,'' in ji Laura.
Wani ma'aikaci Rob Michalak ya bayyana yadda ya ji lokacin da ya fara barci a wurin aiki,'' Ranar farko da na fara barcin sai na ji wani bambarakwai, amma bayan na yi sai na ji ni wasai kamar ban ma zo aiki ba don kwakwalwata ta samu hutu.''
"A karo na biyu na da shiga dakin barcin da ake wa lakabi da Da Vinci Room, na san abin da zan yi yana da kyau kuma bai sabawa dokoki da ka'idojin aiki ba.''

Asalin hoton, MetroNaps
Wata kujera mai kama da gadon asibiti mai malafa da ake kira MetroNaps a Turance, an yi ta ne don mutum ya dan gyangyada idan ya ji barci.
Ana samun irin ta yawancin a wuraren da suke aiki a kullum babu kakkautawa, wato sa'a 24, kamar filin jirgin sama, da asibitoci, da masana'antu, an kuma fara ganinsu a wuraren motsa jiki da jami'o'i.
Lindholm, daya daga cikin ma'aikatan kamfanin da ke samar da MetroNaps, ya ce a lokacin da suka fara mutane sun ga abin kamar wasa, ko don ba a saba gani ba, amma yanzu ana yawan sayanshi musamman a kamfanoni masu zaman kansu.
Wasu na korafin kamfanin ya na son karfafa wa masu barci a wurin aiki gwiwa.











