Shugaban Najeriya Buhari ya taya sabon gwamnan Bayelsa murna

A

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ta dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Bayelsa murnar lashe zaben da aka gudanar ranar Asabar dinnan.

A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan yada labarai Femi Adesina ya fitar, shugaban ya ce wannan "nasara ce mai kayatarwa."

A ranar Asabar din da ta gabata ne aka gudanar da zabukan gwamna a Bayelsa da Kogi.

Sannan hukumar zabe mai zaman kanta INEC, ta sanar da cewa David Lyon na APC ne ya lashe zaben Bayelsa, amma ta ayyana cewa zaben Kogi bai kammala ba.

Shugaban ya yabi magoya bayan APC da 'yan jihar baki daya, ''wadanda suka kada kuri'unsu cikin kwanciyar hankali, duk da 'yan rikice-rikicen da aka samu a wasu wuraren.''

Sanarwar ta kara da cewa shugaban ya yi Allah-wadai da asarar rayukan da aka samu a Bayelsa a lokacin zaben, ya kuma mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan wadanda suka mutun.

"Tashin hankula a lokutan zabe na dakusar da kokarinmu na nuna wa duniya da al'umma mai tasowa cewa mu mutane ne da ke iya zabar shugabanni cikin lumana," a cewar Buhari.

Shugaban ya ce a shirye yake ya yi aiki da sabuwar gwamnati a Bayelsa domin inganta rayuwar 'yan jihar, tare da tabbatar d acewa za a kare rayuka da dukiyoyinsu.Sannan ya nemi sabon gwamnan da ya ci gaba da ayyukan da za su taimaki jihar, ya kuma nemi wadanda ba su amince da sakamakon ba da su bi hanyoyin da suka dace na tsrain mulki wajen kokawa kan hakan.

Zaben Bayelsa bai inganta ba - CDD

Tun da farko a ranar Asabar Cibiyar Demokradiyya da Ci gaba ta Najeriya CDD ta ce yin amfani da aka yi da 'yan bangar siyasa wurin tayar da hankali da sata da kuma lalata kayan zabe a jihar Bayelsa sun raunana duk wani sakamako da zai fito na zaben gwamnan jihar.

A cikin rahoto na farko-farko da ta fitar ta bakin shugabarta Idayat Hassan, CDD ta ce mummunan tashin hankali da aka tsara kuma aka tayar da gangan a rumfunan zabe da dama, sun hana mutane fitowa domin kada kuri'a domin tsira da rayukansu.

A karshen rahoton nata kungiyar ta CDD ta ce da alama zabe a Najeriya ya koma na a-mutu ko a yi-rai, kuma akwai jan aiki gaba kafin a magance wannan matsala.