An raba daloli a zaben Kogi - CDD

Kungiyoyin lura da zabe na nuna damuwa kan zaben Kogi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kungiyoyin lura da zabe na nuna damuwa kan zaben Kogi

Cibiyar Dimokradiyya da ci gaba ta Najeriya CDD, ta ce an yi amfani da kudi fiye da kima a zaben gwamnan jihar Kogi da aka gudanar a yau Asabar.

A wani taron manema labarai da CDD ta gudanar a garin Lokoja, babban birnin jihar ta Kogi ta yi zargin cewa jam'iyyu sun ringa sayen kuri'u a fili a mazabu da dama a fadin jihar.

A wurare da dama a cewar cibiyar, wakilan jam'iyyu ne suke tabbatar da mutum ya zabi jam'iyyarsu, sai kuma su damka masa kudi.

"A mazabar makarantar firamaren LTU a Okene, wakilan jam'iyyu suna tura mutane bayan sun yi zabe, zuwa wajen wani mutum da ke zaune a kan babur, inda suke karbar Naira 2,000 kowannen su.

CDD ta ce jam'iyyun APC da PDP na da hannu a wajen rabon kudi ga masu zabe a sassa daban-daban na jihar ta Kogi.

Haka kuma cibiyar ta yi zargin cewa an karya dokokin zabe da dama inda wasu 'yan banga suka ringa yawo suna kwatar kayan zabe suna tarwatsa mutane.

CDD ta ce ya kamata a sanya alamar tambaya kan sakamakon zaben na jihar Kogi.

Zargin satar akwati

Masu kada kuri'a a kan layi a zaben Kogi
Bayanan hoto, Masu kada kuri'a a kan layi a zaben Kogi

Bayanai sun ce an sace akwatin zabe na mazabar Sanata Dino Melaye na jam'iyyar PDP, jim kadan bayan ya kada kuri'arsa.

Wakiliyar BBC ta ruwaito cewa wasu mutane a cikin motoci biyu ne suka dira a mazabar Ayetoro, inda suka rinka yin harbi a sama da bindiga, sannan daga bisani suka yi awon gaba da akwatin zaben.

Ta kara da cewa an kai wani da aka harba a kafa zuwa asibiti.

'Ina da rahoton an sa a kashe ni'

'Yar takarar gwamnan Kogi a jam'iyyar SDP Natasha Akpoti
Bayanan hoto, 'Yar takarar gwamnan Kogi a jam'iyyar SDP

'Yar takarar jam'iyyar SDP kuma mace tilo da take takarar gwamna a jihar Kogi Natasha Akpoti, ta yi zargin cewa an jikkata wakilan jam'iyyarta sannan kuma 'yan sanda sun yi awon gaba da wasu.

Ta kara da cewa 'yan sanda sun shaida masu cewa ba su suka kama 'ya'yan jam'iyyar ba kuma a saboda haka ne suke zargin cewa dakarun APC ne suka sace su.

"Ina da rahoton cewa gwamnan APC ya sa a kashe ni," in ji Natasha.

Shi ma dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP a zaben gwamnan na jihar Kogi Musa Wada, ya yi zargin cewa shugaban jam'iyyar APC na mazabarsa ya kulla makarkashiyar kai hari tare da sace akwatin zabe.

Ya fadi haka ne jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a mazabar Ayingba da ke karamar hukumar Dekina.

Dan takarar gwamnan jihar Kogi na jam'iyyar PDP Musa Wada
Bayanan hoto, Dan takarar gwamnan jihar Kogi na jam'iyyar PDP Musa Wada

Addini da kabilanci na taka rawa

'Yan takara uku ne dai aka fi jin amon su a zaben gwamnan, wato da gwamna mai ci Yahaya Bello na jam``iyyar APC, da Musa na jam`iyyar PDP da kuma Natasha Akpoti ta jam`iyyar SDP, wadda ta fito daga yanki daya da gwamna Yahaya Bello.

Masana siyasa dai sun ce kabilanci zai yi tasiri sosai a zaben.

Ana gudanar da zaben ne tare da na sanata mai wakiltar Kogi ta yamma
Bayanan hoto, Ana gudanar da zaben ne tare da na sanata mai wakiltar Kogi ta yamma

Yayin da kowane dan takara na ganin cewa shi zai kai labari, Gwamna Yahaya Bello na fuskantar kalubale sakamakon zargin da ake yi cewa ya gaza wajen inganta rayuwar ma'aikata da rashin tabuka abin a-zo-a-gani ta fuskar raya kasa.

Musa Wada kuma kani ne ga tsohon gwamnan jihar Idris Wada, don haka wasu na ganin cewa bai kamata 'yan gida daya su ci gaba da mamayar kujerar mulkin jihar ba.

Natasha Akpoti kuma a cewar masana, za ta fuskanci matsala kasancewar ta mace, saboda wasu ba sa so mace ta mulke su.

Amma kuma ana ganin cewa za ta iya rage wa Gwamna Yahaya Bello kuri'a, kasancewar tana da magoya baya, gashi kuma sun fito daga yanki daya da Yahaya Bello.