Wasu malaman da suka je taron Aisha Buhari sun ce ba maulidi suka je ba

taron addu'o;i

Asalin hoton, Aisha Buhari

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Litinin ne mai dakin shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta kira wani taron addu'o'i na musamman da aka gudanar a fadar shugaban kasa domin neman agajin Ubangiji game da tarin kalubalen da kasar take fuskanta.

Taron dai ya zo ne a daidai lokacin da wani bangare na al'ummar musulmin duniya ke bukukuwan tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAW, abin da ya janyo muhawara kan ko uwargidar shugaban kasar ta shirya taron ne a matsayin wani bangare na bukukuwan maulidi.

Ba maulidi muka je yi ba

Sai dai daya daga cikin malaman da suka halarci wannan taron alaranma Ahmad Sulaiman ya musanta batun da ake yi na cewa sun halarcin taron ne albarkacin ranar maulidi.

A wani rubutu da ya tabbatar wa BBC cewa an yi ne da izininsa, mallam Ahmad ya ce "Taron yi wa kasa addu'a muka je yi fadar shugaban kasa ba maulidi ba."

Malaman da suka halarci taron sun fito ne daga bangarori irin na kungiyar Izala, da Darika, da kuma Ahlus-sunnah.

Muhawara a shafukan sada zumunta

Wasu 'yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta sun rinka muhawara, ganin cewa taron ya hada malamai daga kungiyoyi daban-daban na addinin musulunci na kasar, wadanda ke da banbancin fahimta game da asali ko rashinsa na bikin maulidi.

Sai dai a wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Aisha Buhari kan yada labarai, Aliyu Abdullahi ya fitar, ta ce an shirya taron ne don yin duba kan mahimmancin addu'o'in nemar wa Najeriya ci gaba, ba tare da alakanta shi da bikin maulidi ba.

Amma a lokacin da take nuna rahoton, kafar yada labaran talbijin ta kasa NTA, ta sanya rubutu ta kasa cewa "Ranar Maulud: Aisha ta hada taron addu'ar kasa," duk da dai ba a ambaci haka a rahoton ba.

Amma ba kamar yadda wasu ke yada cewa har da shugaban Izala na kasa da sakataren kungiyar wato Sheikh Bala Lau da Sheik Kabiru Gombe a mahalartan ba, domin kuwa wata majiya mai karfi daga bangaren malaman ta tabbatar wa BBC cewa a lokacin da aka yi taron malaman biyu suna birnin Alkahira na kasar Masar.

Sannan kuma ba a gansu a hotunan mahalarta taron ba.

Labaran NTA

Asalin hoton, Screengrab Youtube

Kauce wa Facebook, 1

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 1

Yi wa malamai shagube

An yi ta yi wa wasu malamai shagube a shafukan sada zumunta, kasancewar sun fito daga bangaren masu sukar Maulidi. Sai dai kuma an samu masu tare wa malaman wannan fada.

Kauce wa Facebook, 2

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 2

Facebook post maulud

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, Duk da ta ba ta alakanta taron da mauluidi ba, wasu da yawa sun dauke shi a matsayin na maulidin
Kauce wa Facebook, 3

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 3

Wannan sakon na sama cewa yake "Wannan ita ce maganar gaskiya, amma duk da haka wasu mutanen na cewa taron maulidi ne. Wacce ta shirya da kanta ta ce taron yi wa kasa addu'a ne."

Wasu daga cikin malaman da suka halarci taron addu'ar su ne Sheikh Ahmed Sulaiman, da Sayyid Ibrahim Dahiru Bauchi, da Sheikh Abdullahi Usman Gadon Kaya, da Sheikh Muhammad Bin Usman, da Sheikh Abdulwahab Abdallah, da kuma Farfesa Ishaq Oloyede.

Karin wasu labaran da za ku so ku karanta:

"Maza ku bai wa iyalansu hakkokinsu"

A jawabin da ta yi a wajen taron, wanda aka yi wa taken ''muhimmancin addu'a wajen saita kasa', Aisha Buhari ta jaddada mahimmancin ibada wadda ta ce kofa ce mara hijabi ta amsa addu'o'i.

Ta kuma tunatar da mahalarta taron kan yadda addinin musulunci ya zayyano nauyin da ke rataye a wuyan kowa, kuma a cewarta, ''dole ne mu sauke wannan nauyi gwargwadon iyawarmu.''

Aisha Buharin ta kuma yi jawabi kan nauyin da ke rataye a wuyan maza, sannan ta bukace su da "su rike koyarwar Annabin tsira, Muhammad SAW wajen kula da iyalansu" wanda ta ce zai iya magance tarin matsalolin da suka addabi Najeriya.

Ta ce matsalolin da ake fama da su a kasar suna da alaka da yadda ''iyaye suka yi sake wajen dora yaransu kan turba mai kyau.''

Malamai a lokacin taron addu'a da uwargidar shugaban Najeriya Aisha Buhari ta shirya

Asalin hoton, FACEBOOK/AISHA BUHARI

Bayanan hoto, Malamai a lokacin taron addu'a da uwargidar shugaban Najeriya Aisha Buhari ta shirya

Uwargidan shugaban kasar ta kuma bukaci al'ummar musulmi da su rika hakuri da juna su kuma zauna cikin aminci da yarda, musamman tsakaninsu da sauran jama'ar da suke da banbancin addini da su.

Kokarin gina al'umma

Game da kokarin gina al'umma kuwa, Aisha Buhari ta ce gwamnati tana fadada hanyoyin samun kudadenta ta bangaren noma da sauran bangarorin da ba na man fetur ba.

A nasa bangaren, shugaban taron kuma babban sakatare na majalisar koli ta addinin musulunci, Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce Najeriya ta tsinci kanta a tsaka mai wuya ta yadda cin hanci kadai ya durkusar da kasar.

Taron dai ya samu halartar shugaban ma'aikata a fadar gwamnatin Najeriya Mallam Abba Kyari da ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, da babban sifeton 'yan sandan Muhammad Adamu da tsohon gwamnan jihar Nassarawa, Sanata Tanko Al-Makura da sauran sanatocin kasar, da matan gwamnoni masu ci da tsoffin gwamnoni da kuma sauran manyan baki.