Hotuna: Yadda aka gudanar da bukukuwan mauludi a duniya

Musulmi a kasashen duniya daban-daban sun gudanar da bukukuwan maulud, inda da dama suka yi tattaki da tarukan yabo ga annabi Muhammad SAW.

India

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mai fafutuka a kasar Indiya, Swami Agnivesh yana daga wa jama'a hannu a lokacin tattakin bikin tuna wa da haihuwar annabi Muhammadu SAW a Mumbai.
India

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yara sun yi wa mota ado da balan-balan lokacin tattakin murnar Mauludi a Mumbai, Indiya.
Dakar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dandazon masu kwanan zaune domin sauraron karatu na murnar mauludin annabi Muhammad SAW, a Dakar na Senegal.
Dakar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani bangare na masu mauludi a birnin Dakar na kasar Senegal.
Tunisia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda masu bikin mauludi suka kawata birnin Kairouan na kasar Tunisia yayin bukuwan maulud.
Indonesia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu musulmi a bakin wani masallaci a garin Yogyakarta na Indonesia yayin bikin maulud.
Lebanon

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda wasu musulmi suka yi ta raye-raye da kade-kade a bikin maulud din a birnin Tripoli na kasar Lebanon.
Indonesia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu bikin mauludi a kasar Indonesia, inda suka dauki wani shuci mai kama karaga domin alamta wani muhimmin abu dangane da ranar Mauludi.
India

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum da dansa kan doki domin bikin maulud a birnin New Delhi na Indiya.
Maulud

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsaffi ke nan ke addu'o'i na musamman a lokacin bukukuwan maulud a yankin Kashmir.
Maulud

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Masu bikin maulud sun yi dandazo a dandalin al-Sabin Square a birnin Sana'a na kasar Yemen.
Malaysia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Daruruwan musulman da suka yi tattaki domin tuna wa da ranar haihuwar annabi Muhammad SAW a birnin Kuala Lumpur na Malaysia.
Ghana

Asalin hoton, Zuriya FM Ghana

Bayanan hoto, Wasu masu tattakin murnar maulud rike da tutokci a birnin Kumasi na Ashanti da ke kasar Ghana.
Ghana

Asalin hoton, Zuriya FM Ghana

Bayanan hoto, Wani bangaren mata masu murnar maulud a birnin Kumasi na Ghana.
Ghana

Asalin hoton, Ghana

Bayanan hoto, Mataimakin shugaban kasar Ghana, Alhaji Mahmudu Bawumia ke gaisa wa da wani malami a wurin bikin maulud a birnin Kumasi na Ghana.
Ghana

Asalin hoton, Ghana

Bayanan hoto, Babban limamin kasar Ghana, Sheikh Dr Usman Nuhu Sharubutu yake addu'o'i a lokacin bikin mauldu a birnin Kumasi.
Abuja
Bayanan hoto, Wani bangaren masu tattakin murnar mauludi a birnin Abuja.
Abuja
Bayanan hoto, Bangaren masu zikiri da rera yabon annabi domin bikin zagayowar ranar haihuwarsa.
Abuja
Bayanan hoto, Sahun 'yan mata 'yan makaranta a lokacin tattakin bikin mauludi a birnin Abuja.
Abuja
Bayanan hoto, Wani bangaren masu zikiri da yabon annabi lokacin jerin gwanon mauludi ranar Litinin a birnin Abuja.