Maina zai gurfana gaban kuliya bayan kwace kadarorinsa 23

A ranar Talatar nan ne dai mai shari'a, Folashade Giwa Ogunbanjo na babbar kotun Abuja ya bayar da umarnin cewa gwamnatin tarayya ta karbe kadarori guda 23 mallakar tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho a Najeriya garambawul, Abdulrasheed Maina.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumar EFCC ke shirin gurfanar da Maina a gaban kuliya ranar Juma'a mai zuwa.

Hukumar za ta tuhumi Abdulrasheed Maina ne da laifuka 12 da suka hada da safarar kudi da amfani da bankin boge da kuma zamba.

Har wa yau, EFCC za ta gurfanar da Faisal Abdulrasheed Maina wadda da ne ga tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho garanbawul din ne bisa tuhume-tuhume irin wadanda ake tuhumar mahaifin nasa.

Mai shari'a Ogunbanjo ya bayyana kwace kadarori mallakar Maina ne sakamakon wata kara da hukumar EFCC ta shigar, inda ta nemi da a mallaka wa gwamnati kadarorinsa na dan wani lokaci har zuwa lokacin da za ta kammala bincike.

Kadarorin mallakin Maina da kwacewar ta shafa sun hada da wadanda ke a Abuja da Kaduna da Sokoto da Borno.

Hukumar ta EFCC dai ta kuma nemi kotu ta sanya sanarwa a jaridu dangane da kwace kadarorin domin bai wa duk mai son kalubalantar kwacewar ya dauki matakin shari'a.

A farkon watan Oktoban nan ne dai mai magana da yawun hukumar DSS, DR Peter Afunnanya ya shaida wa manema labarai cewa jami'an hukumarsa da na EFFCC sun kai samame wani otal inda suka kama Abdurrashid Maina.

Dr Peter ya ce a lokacin da suka je otal din sun samu Mainan ne tare da dansa mai shekara 20 wanda ya yi yunkurin far wa jami'an da wata 'yar karamar bindiga da ke hannunsa, kafin daga bisani su ci karfinsa.

Mai magana da yawun DSS din ya kara da cewa jami'an nasu sun samu bindiga karama da alburusai da mota mai sulke kirar Range Rover da BMW da na'urar daukar hoto daga sama da kuma kudaden kasashen waje duka a tare da Abdurrashid Maina.

Hukumar DSS din ta ce za ta mika Maina tare da abubuwan da aka samu a tare da shi ga hukumar EFCC domin daukar matakin da ya kamata wajen hukunta shi.