'Yan Saudiyya na ce-ce-ku-ce kan harajin taba sigari

Bin Salman

Mutane a Saudiyya na ci gaba da nuna takaici musamman a shafukan sada zumunta bayan da gwamnatin kasar ta fitar da sabbin haraji kan nau'ika daban-daban na taba sigari, abin da a wasu wuraren ya rubanya kudin shan tabar Shisha.

A shafukan sada zumunta mutane sun rinka wallafa rasitan kudaden da suka biya na Shisha, wanda suke bayyana a matsayin wata tatsar al'umma da ta zarce kima.

Akwai dai rashin fahimta kan ko za a rubanya kudaden sauran abubuwa baya ga nau'ikan taba din da aka yi wa wannan kari.

Tuni dai wasu wuraren cin abinci suka jingine sana'ar ta shisha.

A watan Mayu ne dai kasar Saudiyya ta fara aiwatar da haraji kan tabar latironi da kayan zaki da ta fito da su a 2017.

Hukumar Zakka da Haraji ta kasar ce dai ta ce an sa kaso 100 kan tabar latironi da dangoginsu sannan kaso 50 a kan kayan sha masu zaki.

An dora harajin ne kan wasu kayayyaki da ake ganin na da illa ga lafiyar jama'a.

Saudiyya wadda ita ce kasar da tafi kowacce fitar da mai a duniya, ta fito da haraji kan kaya na kaso a watan Janairu 2018.

Tuni dai Asusun Lamuni na Duniya ya yi san-barka da bullo da harajin na kaya inda ya bayyana shi da wata babbar nasara.