'Rashin fahimtar addini ke sa yawan hayayyafa a Niger'

Issoufou

Shugaban jamhuriyar Niger, Mahamadou Issoufou ya ce "rashin fahimtar addini ne" ke sa iyaye ke haihuwa da yawa a kasarsa, kamar yadda jaridar The UK Guardian ta rawaito.

Ya shaida wa jaridar ne yayin wata hira inda ya ce karuwar yawan jama'a a kasar na yi wa kasar tarnaki wajen sauyin yanayi da kuma tattalin arziki.

Niger wadda kaso 98 na al'ummarta musulmi ne na da yawan jama'ar da ya kai miliyan 22.4, al'amarin da ke nuna karuwar yawan jama'ar daga milyan takwas a 1990.

"Muna samun karuwar jama'a da kaso 4 a duk shekara... yawan jama'a zai karu a shekaru 17 masu zuwa. A shekara ta 2050 za mu iya zama kasa ta biyu mai yawan jama'a a nahiyar Afirka bayan Najeriya." In ji Shugaba Issoufou.

Yin amfani da magungunan kayyade iyali ga maza ya rage yawan 'ya'yan da mace za ta haifa zuwa shida.

Alkaluman Bankin Duniya na 2016 sun nuna cewa mace na iya haihuwar yara fiye da bakwai a jamhuriyar Niger.

Shugaba Issoufou ya ce Kur'ani ya fayyace yadda ya kamata iyaye su sauke nauyin da ke kansu ga 'ya'yansu da kuma haifar yaran da za su iya kula da su.

"Kafin zuwan musulunci, ana aurar da mata a shekara 18 to amma saboda rashin fahimtar addinin ya sa ake aurar da kananan yara 'yan shekara 12 zuwa 13. Amma idan muka duba me Kur'anin yake fadi ne? Idan mutum ya karanta Alkur'ani zai fahimci cewa littafin yana magana ne a kan iyaye masu kula da 'ya'yansu. Musulunci ya kafa sharadin cewa haihuwar 'ya'ya da yawa ta ta'allaka ne ga iya tarbiyyantar da ilimantar da su."

Mahamadou Issoufou ya kara da cewa ra'ayinsa kan haihuwar yara da yawa bai ci karo da na malaman addini ba wadanda suke sukar kiraye-kirayen gwamnatinsa na kayyade iyali.