'Mai karfin fada a ji', wane ne Mamman Daura?

Buhari da Mamman Daura

Asalin hoton, Twitter

    • Marubuci, Usman Minjibir
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Za a iya cewa idan akwai wani suna da a yanzu haka ya fi kowanne kai komo a kunnuwan 'yan Najeriya shi ne Mamman Daura.

Shin wane ne Mamman Daura?

BBC Hausa ta tattauna da wasu 'yan uwa da abokansa a garin Daura na jihar Katsina, kan tarihinsa da ma alakarsa da Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

An haifi Mamman Daura a watan Nuwamban 1939 a garin Daura na jihar Katsina. Mamman, kamar yadda ake kiransa, ya yi makarantar firamare a garin na Daura, inda bayan kammala makarantar ya tafi sakandare a garin Okene na jihar Kogi.

Mamman Daura ya kammala sakandare a 1956, inda ya koma gida Daura ya yi aiki da hukumar NA na wasu 'yan shekaru kafin daga bisani ya koma aiki da gidan rediyon Kaduna a lokacin yana karkashin hukumar kula da kafafen watsa labarai mallakar gwamnatin Najeriya. Mamman Daura ya fara aiki a matsayin karamin mai shirya shiri.

A shekarar 1962 zuwa 1968, Mamman ya karanci fannin tsumi da tanadi da kuma sanin makamar mulki a kwalejin Trinity College da ke Dublin a Ireland.

Bayan dawowarsa Najeriya ne ya fara aiki a ofishin tsohon gwamnan soja na jihar Arewa ta tsakiya, Abba Kyari.

A 1969 ne kuma ya koma aiki da kamfanin jaridar New Nigerian da ke Kaduna, inda ya fara da matakin edita kafin daga bisani kuma ya jagoranci jaridar.

Mamman Daura ya zamo mamba a majalisar gudanarwa ta bankin Afirka na Africa International Bank sannan ya shugabanci bankin kasuwanci da masana'antu da ake kira Nigerian Bank of Commerce and Industry a wancan lokaci.

Aisha Buhari

Mece ce alakar Mamman Daura da Buhari?

Mamman Daura da Buhari 'tamkar Hassan da Hussaini suke duk da cewa Mamman ya bai wa Buhari shekara kusan biyar', in ji dan uwa ga mutanen biyu wanda ba ya son mu ambaci sunansa.

Hakan kuwa ya fara ne tun lokacin da mahaifin Buhari ya rasu, al'amarin da ya sa aka mika Buharin ga yayansa, malam Dauda Daura wanda mahaifi ne ga Mamman Daura.

Majiyar tamu ta tabbatar mana cewa ko a wancan lokaci "'yan uwa cewa suke ba a shiga tsakanin Mamman da Buhari" kasancewar komai tare suke yi.

"Tafiyar Mamman makarantar sakandare a Okene, shi kuma Buhari ya tafi Katsina ne lokacin da mutanen biyu suka rabu."

To sai dai kuma "abokan kuma 'yan uwa biyu sun sake haduwa a Burtaniya lokacin da Mamman ya tafi Dublin shi kuma Buhari ya tafi karatun soja a can", in ji majiyarmu.

Bayan Mamman da Buhari sun koma Najeriya "alakarsu ta kara danko."

Buhari da Abba Kyari
Bayanan hoto, Abba Kyari ne shugaban ma'aikatan gwamnatin Buhari a karo na daya da na biyu

Mamman Daura a idon masu sharhi

Masu fashin bakin siyasa a Najeriya irin su Dr ABubakar Kari na yi wa Mamman Daura kallon wani mutum da bai da mukami amma kuma yana da karfin fada a ji a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

"Karfin fada a ji da Mallam Mamman Daura yake da ita a gwamnatin nan ba ta rasa nasaba da alakar Buhari da Daura wadda ta fara tun tale-tale." In ji Dr Kari.

Dr Kari ya kara da cewa "karfin fadar Mallama Mamman Daura" ba yau ta fara ba domin ko a gwamnatin Buhari a zamanin soja, Mamman Daura yana da wasu da ake ganin "yaransa" ne a mukaman ministoci."

Bugu da kari, masanin kimiyyar siyasar ya ce "ba tun yau ba ake yi wa Mamman Daura kallon mai karfin fada a ji a gwamnatoci daban-daban musamman wadda 'yan arewa ke jagoranta.

"Ai tun kafin yanzu, ana alakanta Malam Mamman Daura da wata kungiyar masu fada a ji a arewacin Najeriya da ke juya akalar gwamnatocin da 'yan arewa ke jagoranta. Ana yi wa wannan kungiyar kirari da Kaduna Mafia."

Karfin fada a ji a duniya

Mamman Daura

Asalin hoton, Mamman Daura

Wata kila tambayar da masu bibiyarmu za su yi ita ce shin a Najeriya ne kawai ake samun masu karfin fada a ji duk da cewar ba su da mukami a gwamnati?

Dr ABubakar Kari na jami'ar Abuja na da ra'ayin cewa "ba yanzu aka fara ba. Kuma ba a Najeriya aka fara ba."

Ya ce karfin fada a ji ya fara ne tun lokacin da aka bullo da tsarin dimokradiyya inda jama'a za su zabi jagororinsu.

"A kowacce kasa ana samun sigar masu karfin fada a ji a gwamnati, illa dai na wata kasar na banbanta da na wata."

Dangane da karfin fada a ji a Najeriya, Dr Kari ya ce "tun bayan komawar kasar turbar dimokradiyya a 1999 ake samun irin wannan dabi'a, inda wani walau yana da mukami a gwamnatin ko kuma ba shi da shi amma saboda alakar jini ko ta yanki ko ta addini ko kuma kasancewarsa basarake yana da karfin juya akalar shugaba."

Daga karshe Dr Abubakar Kari ya kwatanta irin karfin fada a ji da Mamman Daura yake da shi a gwamnatin Shugaba Buhari da irin wanda tsohon ministan yada labaran kasar, Cif Edwin Clerk yake da shi a zamanin gwamnatin Goodluck Ebele Jonathan.

Jonathan da Buhari
Bayanan hoto, Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya ziyarci Shugaba Buhari

Tasiri

Dr ABubakar Kari ya ce samun mutane a gwamnatoci da ke da karfin fada a ji ka iya zama alkairi ko sharri ga gwamnati.

Ya ce "idan aka yi sa a masu juya akalar gwamnati na da niyyar alkairi ga kasa, to a nan za a yi san barka da karfin fada a jin da suke da shi amma idan aka yi rashin sa a aka samu masu irin wannan karfi na yin katsalanda ga gwamnati, ta hanyar hana ruwa gudu to irin wannan ba ya zama alkairi ga 'yan kasa ko kuma wadanda ake jagoranta."

Rufewa

Duk da wannan alaka da ke tsakanin Mamman Daura da Shugaba Muhammadu Buhari da kuma irin karfin fada a ji da masu fashin bakin siyasa suka ce Mamman Daura na da shi a wannan gwamnati, a baya-bayan nan wasu alamu sun nuna 'yar rashin jituwa tsakanin iyalan shugaba Buhari da na Mamman Daura.

An sha jin matar Shugaba Buhari a wuraren taruka daban-daban tana yin shagube ga wasu mutane da take zargin sun zagaye mai gidanta hana shi aiki duk da cewa ba ta taba ambatar suna ba.

To sai dai a wata balahira da ta mamaye batun "auren Buhari" da aka yi ta yada wa a kafafen sada zumunta a makon da ya gabata, Aisha Buhari ta kama suna bayan dawowarta daga Landan inda ta koka da wasu abubuwa da ta ce an yi mata na rashin kyautawa amma kuma an kasa yin wani abu a kai kasancewar mai laifin 'yar gidan Mamman Daura ce.

To amma da BBC ta tambayi Fatima Mamman-Daura ko tun can dama ana samun rashin jituwa tsakanin Mamman-Daura da Aisha Buhari? Sai ta bayyana cewa "kafin Shugaba Buhari ya hau kan karagar mulki, suna zumunci lafiya kalau, amma tun bayan nan ne komai ya sauya aka fara samun matsaloli."

Dangane kuma da tambayar da aka yi mata bisa zarge-zargen da 'yan kasar suke da shi na cewa mahaifinta ya kanaine Shugaba Buhari sai ta ce "ba gaskiya ba ne."