Wani kamfani ya yi barazanar rufe babban bankin Najeriya

Wani kamfanin kasar waje ya gargadi gwamnatin Najeriya cewa zai dakatar da babban bankin kasar idan har bai biya shi diyyar da kotun koli ta umarci a ba shi ba.

Wasu takardu da sashen BBC Pidgin ya gani sun nuna cewa kotun kolin ta umarci babban bankin da ya biya kamfanin sadarwa na Interstella Communications dala miliyan 260 saboda saba yarjejeniyar da ya kulla da kamfanin sadarwar.

Lauyan kamfanin, Nnadi ya ce sun yi matukar mamakin yadda babban bankin ya yi biris da umarnin kotun koli har tsawon shekaru biyu.

A yanzu kamfanin na jira diyyar dala miliyan 285 idan aka hada da kudin ruwa.

Kamfanin ya ce ya sha rubuta wa babban bankin takardar neman hakkinsa amma bai taba samun amsa ba.

A shekarun da su ka gabata ne kamfanin Interstella Communications ya kulla yarjejeniyar adana bayanai da gwamnatin Najeriya, to amma daga baya ya fahimci cewa an soke yarjejeniyar ba tare da sanin sa ba, wanda hakan ya sa ya garzaya kotu.

Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin shekara daya da wani kamfanin kasar waje ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta biya shi diyyar makudan daloli bisa dalilan saba yarjejeniya.

Ba a jima ba da wani kamfanin kasar waje da ke samar da iskar gas (P&ID) ya yi nasara a kan gwamnatin Najeriya a wata shari'a da aka gudanar a Burtaniya, bayan da kotu ta umarci gwamnatin da ta biya shi dala biliyan tara kan saba yarjejeniya.

To sai dai mai magana da yawun babban bankin Najeriya, Isaac Okonkwo ya fada wa sashen BBC Pidgin cewa lauyoyinsu sun tabbatar cewa bankin ba shi da alhakin biyan kamfanin ko sisi.

Ya kuma kara da cewa ba shi da hannu kai tsaye a kan yarjejeniyar da kamfanin ya kulla da gwamnati.