Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wenger zai dawo fagen daga, Allegri na son horas da United
Tsohon mai horas da 'yan wasan Juventus Massimiliano Allegri na son ya yi aiki tare da tsohon mai tsaron bayan Manchester United Patrice Evra, idan har ya samu aikin horas da kungiyar in ji Jaridar Daily Mail.
Daya daga cikin masu hannun jari a kulob din Manchester United Kevin Glazer na shirin sayar da kaso 13 da ya mallaka in ji The Sun.
Tsohon mai horas da kulob din Chelsea Maurizio Sarri na son mai tsaron bayan Italiya Emerson Palmieri da dan wasan tsakiyar Chelsea Ngolo Kante su bar Chelsea zuwa Juventus a cewar Daily Express.
Haka ma Sarri na son kawo dan wasan tsakiyar Tottenham Christian Eriksen ta hanyar musaya da dan wasan tsakiyar sa Adrien Rabiot kamar yadda Le 10 Sport via Mirror ta ruwaito.
Kulob din AC Milan na son sayen dan wasan tsakiyar Arsenal Muhammad Elneny mai shekaru 27, da yanzu yake wasa a matsayin aro a kulob din Besiktas na Turkiyya a cewar Gacetta- in Italian .
Tsohon mai horas da yan wasan Tottenham Harry Redknapp ya ja kunnen Mauricio Pochettino da ka da ya yi gangancin barin kulob din zuwa Manchester United, la'akari da shekarun da kulob din ke bukata kafin ya dawo kan ganiyarsa in ji The Mirror.
A wata mai kama da haka Man U na fatan Juventus za ta karbi tayin fam miliyan tara ga dan wasan ta Mario Mandzukic in ji Goal.com.
Daily Express ta ruwaito cewa Chelsea ta shiga cikin jerin kungiyoyin da ke neman Charlie Allen, matashin dan wasan tsakiyar Ireland ta Arewa mai shekaru 15.
Ita kuwa ESPN cewa ta yi mai tsaron bayan Man U Victor Lindelof ya ce bai mayar da hankali kan rahotannin da ke cewa kulob din Barcelona na zawarcin sa ba.
A wata mai kama da haka Manchester United za ta bai wa mai horas da kulob din Ole Gunner Solskjaer goyon baya wurin sayen yan wasa a watan Janairu.To sai dai kulob din ya sanar cewa ba zai kashe kudin da suka wuce kima ba don fita daga matsin da suke ciki.
Dan gaban Paris St. German Neymar zai yi jinya har tsawon sati hudu in ji Mirror.
A karshe London Evening Standard ta ruwaito cewa tsohon mai horas da 'yan wasan Arsenal Arsene Wenger zai dawo fagen horas da tamaula a badi, da zarar an kaddamar da littafi kan tarihin rayuwarsa.