Rikicin Ganduje da Sarki Sanusi ya fara cin rawuna

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ma'aikatan fadar Kano kuma Dan buram din Kano, Alhaji Manniru Sunusi ya musanta sauke Malam Auwalu Idi daga mukaminsa na Maja Sirdin sarki.
Kula da dawakin Sarkin na kano na karkashin ofishin Maja sirdi, sai dai Malam Auwalu ya ce tun hawan Sarkin na yanzu, Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya nuna masa rashin amincewa.
Hakan kuma ya sa Sarkin ya mayar da ayyukan na maja sirdi karkashin Shamakin Kano.
Sai dai a wata hira da BBC, shugaban ma'aikatan fadar ya musanta batun korar Maja sirdin tare da umartar sa da ya bar gidan da yake zaune sama da shekara 30 a cikin fadar.
Masarautar ta kuma yi zargin cewa a kwanan baya wani sirdi ya bata, kuma an ga wasu abubuwan da ba dai-dai ba, shi ya sa shamakin ya mayar da kula da kayayyakin karkashinsa.
Haka kuma masarautar ta musanta cewa an kori Maja sirdin ne saboda zargin shiga harkar siyasa, bayan ya bai wa gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje kyautar babbar riga.
A ranar larabar da ta gabata ne Maja sirdin ya yi kyautar rigar don taya gwamna Ganduje murna kan nasarar da ya samu a kotun sauraron korafe-korafen zabe ta jihar.
Haka kuma an ce an ga wasu abubuwa da ke dauke da hotunan tsohon sarkin na Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero hannun Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana dagawa, abin da aka zargi Maja sirdin da bai wa gwamnan.
Masu nazarin al'amuran da ke faruwa a jihar dai na ganin zaman 'yan marinar da ke tsakanin fadar gwamnatin jihar da kuma masarautar ya yi kamari ne tun lokacin da gwamnan ya raba masarautar gida biyar.
Wasu na nuna fargabar cewa gwamnan ya yi hakan ne domin sauke Sarki Sanusi daga mukaminsa ta hanyar sauya masa masarauta.
Gwamnatin jihar dai ta sha musantawa.












