An fara sulhu tsakanin Sarki Sanusi da Ganduje

Gwamnan Kano da Sarki Sanusi

Asalin hoton, Tanko Yakasai

Gwmanatin Ganduje ta ce tana ci gaba da binciken masarautar Kano duk da tattaunawar sulhu da bangarorin biyu suka soma tsakaninsu.

Bangaren gwamnatin Kano ne ya tattabatar da cewa an fara tattaunawar sulhu tsakaninsu da masarautar jihar.

Daraktan yada labarai na Ganduje, Aminu Yassar ya shaida wa BBC cewa an yi mitin da sarki da daddare a Abuja.

"An tattauna abubuwa da suka shafi wannan tashin tashina da sauran abubuwa da suka shafi ci gaban Kano," in ji shi.

Ya ce kungiyar gwamnoni Najeriya da Alhaji Aliku Dangote ne suka shiga tsakani suka shirya tattaunawar saboda bukatar tabbatar da ganin an samu daidaito tsakanin shugabannin jihar ta Kano.

Sai dai babu cikakken bayani game da abin da aka tattauna da kuma matsayar da aka cimma.

A ranar Litinin ne dai hukumar karbar korafe-korafen jama'a ta Kano, ta ce Sarki Sanusi ya yi bushasha da kudin masarauta inda kuma ta nemi da a dakatar da shi.

Daga baya kuma, Gwamnatin jihar Kano ta ba Sarki Sanusi awa 48 da ya bayar da bahasin yadda ya kashe kudaden masarautar da ake zargin an kashe ba bisa ka'ida ba.

Zaman sulhun dai tsakanin bangarorin biyu bai sa an fahimci juna ba, kamar yadda Aminu Yassar ya ce yanzu tattaunawar sulhun ce aka fara.

Ya nanata cewa, "ba a daidaita ba, amma bangarorin biyu sun amince su ci gaba da aiki tare don a samu zaman lafiya tsakanin al'umma.

"Sun yi alkawalin za su ci gaba da mutunta juna, domin shugabanni su yi aiki tare don ci gaban jama'a."

Sai dai kuma duk da wannan matakin, amma batun umurnin da gwamnati ta ba Sarki Sanusi na ya mayar da bahasi kan tuhumar yin bushasha da kudaden masarauta na nan.

Kuma batun karar da bangaren masarauta ya kai kotu na nan.

Ya kara da cewa har yanzu gwmanti na ci gaba da binciken masarautar ta Kano kan yadda aka kashe kudadenta kimanin naira miliyan dubu dari uku da miliyan dari hudu.