'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro a Nijar

A kalla jami'an tsaro biyar ne aka kashe lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari a garin Abare na jihar Tillabery mai fama da matsalar tsaro da ke iyakar Nijar da Mali.

Rahotanni sun bayyana cewa ranar Asabar ne wasu mutane kan babura da yawansu ya haura sittin suka afkawa runduna ta musamman ta Gendarmerie dauke da manyan bindigogi.

Lamarin dai ya faru ne a ranar da ake cin kasuwar garin.

Wata majiya ta ce da misalin karfe 5 na yamma, bayan an tashi daga kasuwar ne jami'an tsaron suka afka wa kwanton baunar maharan, inda kuma aka fara harbin kai mai uwa da wabi.

'Yan bindigar sun yi amfani da mata da yara don kare kansu, wanda hakan ya sanyaya gwiwowin jami'an tsaron ya sa su taka tsantsan wajen maida martani a lokacin da 'yan bindigar ke ta sakin wuta.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron Gendarmerie biyar ne suka rasa rayukansu, yayin da maharan suka yi awon gaba da gawarwakin 'yan uwansu da wadanda suka yi rauni.

Wata majiyar hukumar Gendarmerie ta ce maharan sun samu goyon bayan mazauna garin, inda ta tabbatar da faruwar lamarin ba tare da yin wani cikakken bayani ba kan adadin wadanda suka mutu.

A jamhuriyar Nijar dai hare-haren ta'addanci sun yi sanadiyar salwantar rayukan fararen hula dama.

Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa daga watan Janairun 2019 zuwa Agusta, an kashe fararen hula 250 tare da garkuwa da wasu 240 musamman a jihohin Diffa dake kudu masu gabascin kasar da Tillaberi da Tahoua da ke Yammacin kasar.

Rahoton ya kuma bayyana cewa a Tillabery da Tahoua masu iyaka da Mali, an kai hari sau 79 kuma na kashe mutane 42 yayin da 42 suka jikkata, 15 kuma sun yi batan dabo.

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya sha yin kira ga kasahen turai da Majalisar Dinkin Duniya kan a sa wa kasar hannu a yakin da take da masu tada kayar baya.

Sai dai kasancewar dakarun kasashen waje irin su Faransa da Amurka da Jamus da Nijar da na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali bai sa an kawo karshen ta'addanci da hare-haren da kasar ta Nijar ke fuskanta ba.