Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ya dace manyan sojoji su rika bin hanyar Kaduna ta mota'
Masu sharhi a Najeriya na ci gaba da kira ga shugabannin jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sandan kasar da su rika bin hanya maimakon jirgin kasa.
Wannan dai na zuwa ne kwana daya bayan da kakakin majalisar dattawan Najeriya Ahmed Lawan ya yi kira ga manyan hafsoshin da su rika bin hanyar Kaduna zuwa Abuja da mota a madadin jirgin kasa.
Bashir Hayatu Jantile, wani mai sharhi ne a kan al'amurran yau da kullum, inda ya ce "jirgin nan an yi shi ne domin talaka ya samu sauki, amma saboda tsoro kowa da kowa na shiga cikin jirgin"
Mai sharhin na ganin cewa idan hafsan sojojin na bin hanyar to garkuwa da mutane da ke aukuwa a kan hanyar zai saukaka.
"Idan a ce hafsan sojojin kasa idan zai je Kaduna zai hau mota ya tafi, ko hafsan sojojin sama, duk da yana da jirage, idan zai je Kaduna zai hau mota ya tafi, ko kwamishinan 'yan sandan Kaduna idan zai je Abuja zai hau mota, duk wannan sai ya saukaka."
Ana ci gaba da sace daruruwan mutane a kan hanyar ta Kaduna zuwa Abuja mai misalin nisan kilomita 200 duk da kai daruruwan jami'an tsaro domin kawo karshen al'amarin.