Wani mutum ya kashe 'yan sanda 4 da wuka a Paris

Wani mutum mai wuka ya kashe 'yan sandan hudu ne a hedikwatar 'yan sandan da ke a Paris.

Mutumin da ya kai harin da ba a san sunansa ba, an gano cewa ma'aikaci ne a hedikwatar, bayan da 'yan sanda suka harbe shi har lahira.

Har yanzu babu wan jawabi a hukumance. 'Yan sanda sun kulle unguwar ta île de la Cité wadda take a tsakiyar Paris.

Harin ya zo ne kwana daya bayan da 'yan sandan kasar suka yi yajin aiki saboda irin hare-haren da ake kai masu.

Lamarin ya auku ne da misalin karfe daya na rana agogon Faransa a ofishin nasu.

Shugaban kasa Emmanuel Macron da Firai minista Edouard Philippe da kuma ministan cikin gida Christophe Castaner duka sun ziyarci wurin.

Gwamnan Paris Anne Hidalgo ya tabbatar da aukuwar lamarin a shafin cewa "mutane da dama" sun rasu sakamakon harin wanda ya auku kusa da wani babban wurin yawon bude ido wanda ke kusa da babbar mujami'ar Notre-Dame.

A cewar jaridun kasar, mutumin da ya kai harin wani mai shekara 45 ne wanda ya kwashe shekara 20 yana aiki da rundunar 'yan sandan kasar.