Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zan sa kafar wando daya da masu kalaman kiyayya – Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin sanya kafar wando daya da masu kalaman kiyayya.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne ranar Talata lokacin da yake gabatar da jawabinsa na bikin zagayowar ranar samun 'yancin kan kasar.
Najeriya ta samun 'yancin kanta daga turawan mulkin mallakar Burtaniya ranar daya ga watan Oktoba, 1960, wato shekara 59 ke nan.
A jawabin da ya gabatar ga 'ya kasar ta talbijin din Najeriya da misalin karfe 7:00 na safe, shugaban mai shekara 76, ya ce gwamnatinsa ta sha alwashin kare hakkin kowanne dan kasar.
"Hankulanmu sun karkata kan laifukan da suka shafi intanet ta hanyar yada kalaman kiyayya a shafukan sada zumunta," in ji Shugaba Buhari.
"Yayin da muke kokarin kare hakkin kowanne dan kasa game da fadar albarkacin baki da kuma taruka, idan hakan ya sanya wani ya nemi ya tauye wa wani dan kasa nasa hakkin ko kuma kawo wa tsaron kasa cikas za mu dauki tsattsauran mataki a kansa."
Ya yi jawabi mai tsawo cike da bayanai game da manufofi da kuma abin da gwamnatinsa ta APC ta cimma a tsawon shekara hudu da suka shafe da kuma abin da za su yi a wasu hudu masu zuwa.
Kasuwanci da tattalin arziki
Shugaba Buhari ya nuna cewa duk da Najeriya tana mutunta yarjejeniyar tsakaninta da kasashen Afirka da duniya baki daya, kasar za ta yi bakin kokarinta wajen hana yin fasa kwaurin kayayyakin da ba su dace ba zuwa cikinta.
Da alama Shugaban yana magana ne kan rufe iyakokin Najaeriya da aka yi na baya-bayan nan tsakaninta da kasashen Nijar da Benin.
"Yayin da muke mutunta yarjejeniyar kasuwanci tsakaninmu da kasashen Afirka da na duniya, ba za mu yi dari-dari ba wurin yin duk abin da ya dace domin dakile fasa kwauri da shigowa da kayayyakin da suke barazana ga samar da ayyuka a kasarmu."