Ba mu rufe iyakar Najeriya da Benin ba – Hukumar Kwastam

Hukumar Kwastam a Najeriya ta ce ba ta rufe iyakar kasar ta kasa da makwabciyarta jamhuriyar Benin ba.

Mai magana da yawun hukumar Joseph Attah ya ce mutane suna da damar shiga da fita kasar matukar suna da dalilin yin hakan.

Ya ci gaba da cewa sanarwar da aka fitar ga manema labarai kwanakin baya ta ce wani aikin sintiri ne da ake yi a kan iyakar yake haddasa cunkoso, amma babu wani lokaci da aka taba rufe iyakar.

Sai dai tun da farko wasu 'yan kasuwar da ke hada-hada a kan iyakar sun nuna rashin jin dadinsu game da al'amarin.

Ma'ajin dillalan kungiyar fiton kayayyaki a kan iyakar Alhaji Zubairu Mai Mala ya ce su 'yan kasuwa yanzu harkokinsu sun tsaya cak.

Mista Attah ya ce aikin sintirin wanda aka yi masa lakabi da Ex-Swift Response zai kare kasar daga "ayyukan ta'addanci da fashi da makami da fasa kwaurin kayayyaki da shigowa da kananan makamai kasar."

Aikin sintirin na hadin gwiwa ne da hukumar da ke kula da shige da fice da 'yan sanda da hukumar kwastam da sauran jami'an tsaron Najeriya, a cewar sanarwar.

Kazalika, Mista Attah ya ce za a kwashe tsawon kwanki ana aikin sintirin.