AfCFTA: Buhari ya amince da tsarin ciniki maras shinge

Rattaba hannun da Shugaban Najeiryar ya yi kan wannan yarjejeniyar kasuwanci maras shingen za a iya cewa ta kara wa sauran kasashen da ke tuni suka sa hannu karfin gwiwa, kasancewar Najeriyar ce babbar kasuwa saboda yawan jama'a.

Yarjejeniyar ta AfCFTA dai ta samu cikas a bara lokacin da Najeriya ta fice 'yan kwanaki kafin ta sa hannu.

Sai dai kwamitin da gwamnatin ta kafa don tantance tasirin shiga gamayyar ya ba da shawara a makon jiya cewa kamata ya yi Najeriya ta yi tunanin shiga.

Bayanai sun ce ban da Najeriya, kasashen Eritriya da Benin su ma sun zabi janye jiki daga yarjejeniyar.

A ranar Talata ne dai a wata sanarwar da ta wallafa a shafinta na Twitter Fadar shugaban Najeriya, ta ce za ta yi nazari kan yarjejeniyar domin cin moriyar tattaunawar da ake yi da nufin samun kariyar da ta wajaba ga matsalolin fasa-kwauri da kuma jibge wa kasashen Afirka shara.

Sanarwar fadar shugaban Nijeriya ta ambato Muhammadu Buhari na cewa domin samun nasarar yarjejeniyar ciniki maras shinge ta Afirka, jazaman ne sai sun bullo da manufofin da za su bunkasa sarrafa kayan Afirka.

Don haka Afirka ba kawai manufar ciniki take bukata ba, har ma da wani tsarin sarrafa kaya a masana'atun nahiyar.

Ya kara da cewa matsayinsu a sauk'ak'e yake, suna goyon bayan kasuwanci maras shinge matukar za a yi shi cikin adalci kuma a aiwatar da shi bisa doron raba daidai.

Wace riba Najeriya za ta ci daga yarjejeniyar?

Manufar yarjejeniyar ita ce kawar da haraje-haraje tsakanin kasashen nahiyar Afirka tare da kafa wata kasuwa wadda mutum biliyan daya da miliyan 200 ke ci.

Haka kuma za ta taimaka wajen juya jimillar sama da dala tirliyan 2.2 na kayan da ake sarrafawa a nahiyar.

Yanzu haka Najeriya za ta amfana daga wannan salo na kasuwanci ta hanyar fitar da shigar da kaya zuwa kasuwannin sauran kasashen Afirka.

To sai dai da dama daga cikin 'yan kasar na bayyana fargaba kan salon kasuwancin na bai daya wanda a ganinsu zai haifar da rashin daidaito wajen samar da ayyukan yi da kuma a fannin yin kayayyaki.

A baya dai Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa kan barin makwabtan kasashe su je su cika Nijeriya makil da kayayyaki masu rangwamen farashi.

Hakan a ganin shugaban ka iya lalata kokarin karfafa gwiwar farfado da masana'antun kasar da suka durkushe har ma da bunkasar noma.

Yanzu haka ita wannan yarjejeniyar ta kasuwanci ba tare da shinge ba za ta bude wa sauran kasashen nahiyar Afirka kofa ga kasuwannin Najeriya.

Sannan nahiyar za ta samu karfin fada a ji har ma a zauna a teburin tattaunawa kan kasuwanci da sauran nahiyoyin duniya.

Yadda yarjejeniyar AfCFTA take

Tarayyar kasashen Afirka ta AU ce ta fito da wannan yarjejeniyar ta kasuwanci maras shinge wadda kuma kasashe 44 daga kasashen tarayyar 55 suka rattaba wa hannu ranar 21 ga watan Maris 2018 a birnin Kigali na Rwanda.

A 2013 ne aka fara tattauna batun samar da wannan yarjejeniya, inda Tarayyar AU ta jagoranci zaman tattaunawa a 2015.

An yi zaman farko a watan Fabrairun 2016, inda daga nan kuma aka yi wasu zaman har karo shida kafin daga bisani a karkare magana a taron kolin da Tarayyar AU ta yi a birnin Kigali, a watan Maris 2018.

Yarjejeniyar ta nemi da kasashen da suka rattaba hannu su cire kaso 90 na harajin kayayyaki da sana'o'i a fadin nahiyar.

Kungiyar Tattalin arzikin kasashen Afirka ta yi hasashen cewa kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar zai bunkasa da kaso 52 daga yanzu zuwa shekara ta 2022.