Mun kashe sojojin Najeriya biyu - ISWAP

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar IS reshen yammacin Afirka wato ISWAP ta fitar da wani bidiyo da ya nuna yadda mayakanta suka kashe wasu mutum biyu da ta ce dakarun sojin Najeriya ne.
Kungiyar ta ce ta cafke sojojin ne a farkon watan da muke ciki yayin da mayakanta suka kai hari wani barikin soji a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Faifai bidiyon da kungiyar ta fitar a ranar Lahadi na zuwa ne bayan da rundunar sojin Najeriyar ta bayyana cewa sojojin nata na samun galaba a yakin da kasar ke yi.
Rundunar ta ce sakamakon tsaurara hare-hare a kan 'yan kungiyar, mayakan na Boko Haram na tsere wa daga yankin tafkin Chadi zuwa yankunan Sudan da wasu kasashen Afirka.
Ko a ranar Lahadin da ta gabata rundunar sojin kasar ta bayyana cewa ta fara wani aikin tantance shaidar mutane a yankin arewa maso gabashin kasar domin samun bayanai da ke cewa 'yan Boko Haram na shiga al'umma su fake.
Har wa yau, a watan Mayun da ya wuce ma kungiyar ta fitar da wani bidiyo da ya nuna yadda ta halaka mutum tara da ta ce dakarun sojin Najeriya ne.
Kawo yanzu dai rundunar sojin Najeriya ba ta tabbatar da ikirarin na Boko Haram da ke cewa mutanen da ta kashe sojojin ta b ne.







