Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Nijar za ta kashe $4b wajen shimfida bututun mai
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta rattaba hannu kan yarjejeniyar shimfida bututun mai a kan dalar Amurka biliyan hudu da miliyan dari biyar da wani kamfanin China mai sarrafa albarkatun mai.
Ministan Mai na Nijar, Foumakoye Gado ya ce aikin shimfida bututun da za a dauki watanni 42 ana yi, zai kai tsahon kilomita dubu biyu da zai taso daga rijiyoyin Agadem da ke kudu maso gabashin kasar zuwa tashar jiragen ruwan Seme a jamhuriyar Benin.
Wannan aiki na bututu wanda zai ratso jihohin kasar guda uku da suka hada da Zinder da Maradi da kuma Dosso, zai bai wa gwamnatin kasar damar fitar da danyen man da zai kai ganga 110,000 kowace rana daga shekara ta 2021 zuwa kasuwannin duniya.
Alhaji Moustapha Kadi daga kungiyar CODDAE, cewa ya yi abin alfahari ne ga Nijar da ma 'yan kasar ta yadda aka samu wannan dama ta zuba hannayen jari har dalar Amurka biliyan shida da miliyan dari takwas don bunkasa fannin albarkatun mai, a cewarsa.
Daga lokacin da aikin zai kankama zuwa 2031, za a rika samun damar fitar da jumullar gangar mai miliyan 844.8 (a tsawon wannan lokaci) da rijiyoyin na Agadem suka kunsa.
Har ila yau Sadick Ali na kungiyar MITRAD na da yakinin cewa da wannan aiki kasar za ta mike.
Daga shekarar 2025 har zuwa 2030 Nijar za ta rika fitar da ganga 500,000 kowace rana.
Tun a shekarar 2011 ne kasar Nijar ta fara hako man ta da Kamfanin kasar Sin na CNPC ke aikin hakowa daga Rijiyoyin Agadem inda ake tace shi a matatar garin Dan Baki da ke samar da ganga 20, 000 kowace rana.