Ma'aikaci ya shekara 30 yana cin albashi tudu uku

Asalin hoton, Getty Images
'Yan sanda a jihar Bihar ta kasar Indiya na neman wani mutum ruwa a jallo da ake zargi da cin albashin ayyukan gwamnati daban-daban har uku na tsawon shekara 30.
An dauki Suresh Ram a matsayin injiyan gine-gine da kuma karin ayyuka biyu a sashen albarkatun ruwa a lokaci guda a wurare mabambanta.
Mahukunta sun ce Suresh har ma yana dab da yin ritaya daga ayyukan uku rigis.
Sai dai babu tabbaci ko yana zuwa wajen ayyukan amma dai yakan samu karin matsayi.
An dai gano wannan zambar ne jim kadan bayan kaddamar da wani shirin bai-daya a aikin gwamnati.







