Ko Najeriya ta rabu da cutar Polio?

Polio
Bayanan hoto, Likitoci dai sun jima suna kokarin yi wa mutane riga-kafin polio

Najeriya ta cika shekara uku ranar Laraba nan ba tare da samun wani mai dauke da kwayar cutar polio ba.

Wannan ranar dai tana da muhimmancin gaske kasancewar a tsarin hukumar lafiya ta duniya (WHO), dole sai kasa ta shafe shekara uku ba tare da kamuwa da cutar ba kafin a iya ayyana ta a matsayin wacce ba kwayar polio a cikinta.

Amma har yanzu ba a tabbata cewa babu polio a Najeriya ba.

Dole sai WHO ta gudanar da bincike domin tabbatar da lamarin kafin su iya bayyana cewa ba a samu bullar cutar a cikin shekaru uku ba a kasar.

Ba a sa ran cewa hakan zai faru kafin farkon shekara mai zuwa, a cewar shugaban kwamitin polio a Najeriya, DoktaTunji Funsho.

A shekarar 2012, Najeriya na da a kalla mutum 223 da suka kamu da polio wato rabin adadin wadanda ke da polio duk duniya kenan a cewar WHO.

Dokta Funsho ya alakanta wannan nasarar da raguwar rikice-rikice da ake yi da mayakan kungiyar Boko Haram.

Rikicin da ake yi da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya ne ya sa magunguna ba sa isa wasu yankunan jihar Borno.

Borno dai ita ce jiha wacce aka fi samun mutanen da suka kamu da Polio. A ranar 21 ga watan Augustar shekarar 2016 ne aka samu mutum na karshe wanda ya kamu da polio.