Amitabh Bachchan: 'Yadda muka yaki cutar Polio a Indiya'

Amita Bachchan

Asalin hoton, India TV

Bayanan hoto, Amita Bachchan ya dade yana haskakawa a fagen fina-finan Indiya

Shahararren jarumin fina-finan kasar Indiya, Amitabh Bachchan, ya ce sai da Indiya ta shafe shekara takwas kafin ta kasance ba a samu bullar cutar shan inna wato polio ba a cikinta.

Jarumin ya ce, yana mai matukar farin ciki da alfahari kasancewa ya bayar da gudunmuwa wajen kai wa ga wannan mataki a kasarsa.

A shekarar 2014 ne, hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ayyana kasar Indiya a matsayin kasar da ba bu cutar polio a cikinta.

A shekarar 2002 ne, Amitabh, wanda ke da kimanin shekara 75 a duniya a yanzu, ya zama jakadan asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, wajen gangamin kawar da cutar Polio a Indiya.

Amitabh ya ce, "a lokacin da muka fara gangamin wayar da kan mutane a kan illar cutar, ba mu samu nasara ba, saboda mutane ba su fahimci sakon da muke son isar musu ba."

"Sai da na rinka yin kamar wasan kwaikwayo ina nuna kai na a matsayin dattijon da ke nuna fushinsa a kan yaran da ba a yi wa allurar rigafin cutar Polio ba."

Ya ce, haka ya rinka fakewa da yana fushi da iyayen da ba su yarda an yi wa 'ya'yansu rigafin cutar ta Polio ba.

A cikin wata sanarwa da aka fitar, Amitabh ya ce, matakin da ya dauka na kasancewa dattijo mai fushi da yaran da ba a yi wa rigafin cutar polio ba, ya taimaka matuka gaya wajen samun nasarar ganganmin wayar da kan mutane da suka yi.

Amita ya ce ' Babban abin alfahari ne a gare ni kasancewar na bayar gudunmuwa wajen kawar da cutar polio a kasata'.

Wannan layi ne

Wane ne Amitabh Bachchan?

Amita Bachchan

Asalin hoton, Rotten Tomatoes

Amitabh Bachchan dai fitaccen jarumi ne da ke fitowa a fina-finan Indiya, wanda kuma al'ummar kasar ke ganin kimarsa da bashi girma.

An haife shi a ranar 11 ga watan Oktobar 1942.

Ya yi suna ne a shekarun 1970s, sakamakon fitattun fina-finan da ya yi kamar Zanjeer da Deewaar da kuma Sholay,

Ya fito a fina-finai sama da 150.

Ya samu lambobin yabo da dama sakamakon rawar da ya ke takawa a fina-finai.

Karin wasu labaran da za ku iya karantawa