Iran ta sake 'kwace jirgin da ke fasa-kaurin mai'

Stena Impero

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Har yanzu Iran na tsare da jirgin Stena Impero mallakar Burtaniya

Kasar Iran ta sake tare wani jirgin dakon mai na kasashen waje a yanking Gulf, kamar yadda gidan talbijin din kasar ya sanar.

An rawaito kwamandan sojojin kundumbala na juyin juya-halin kasar yana cewa sojojinsu na ruwa ne suka "kwace jirgin mai dauke da mai domin yin fasakauri zuwa wasu kasashen labarawa", a yankin Gulf.

Ya ce jirgin na dauke da litar mai dubu 700, inda ya kara da cewa sun kuma tsare matuka jirgin guda bakwai.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya kan jerin takunkuman da Amurka ta kakaba wa man kasar Iran.

Amurka ta sanya takunkuman ne dai bayan da ta sanar da ficewa daga yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu a 2015 kan dakatar da ayyukan samar da makaman nukiliyar iran.

Wannan ne karo na biyu da Iran take zargin wani jirgin ruwa da fasakaurin mai.

A watan da ya gabata ne dai Iran ta kwace jirgin kasar Burtaniya a ruwan in the Strait of Hormuz.

Amurka ta dora alhakin kai harin bam a kan wasu jiragen dakon mai guda biyu a yankin Gulf a watannin Mayu da Yuni, zargin da Iran din ta sha musantawa.

Latsa alamar bidiyo da ke kasa domin kallon yadda sojojin Iran suka "kwace jirgin da ke fasa-kaurin mai".

Bayanan bidiyo, Iran ta saki bidiyon yadda aka kwace jirgin da ke fasakaurin mai