Buhari ya fitar da sunayen sabbin ministocinsa

Asalin hoton, Sadiya Farouk Twitter
Shugaba Muhammadu Buhari ya fara fitar da sunayen sabbin ministocinsa.
Bakwai daga cikin ministocin mata ne, kashi 16% kenan wanda kasa da kashi 35% ne da masu fafutika ke bukatar gani a cikin gwamnatin.
Mai bai wa shugaban shawara kan harkokin sada zumunta Bashir Ahmad ne ya fara wallafa sunayen a sahafinsa na Twitter a ranar Talata.
Daga cikin sunayen da aka fitar zuwa yanzu akwai tsofafin minsitocinsa akwai kuma sunayen sabbin mutane da a baya ba sa cikin majalisar zartarwar shugaban.
Tuni dai shugaban kasar ya aike sunayen ga majalisar dattijai domin tantancewa.
Sunayen sababbin ministoci a karon farko
- Sheikh Isa Ali Pantami - Gombe
- Sanata Godswill Akpabio - Akwa Ibom
- Alhaji Sabo Nanono - Kano
- Gbemi Saraki (Kanwar tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki) - Kwara
- Rauf Aregbesola tsohon gwamnan - Osun
- George Akume - tsohon gwamnan - Benue
- Timipre Sylva - tsohon gwamnan - Bayelsa
- Sadiya Farouk - Zamfara
- Maryam Katagum - Bauchi
- Ramatu Tijjani - Kogi
- Sanata Olorunnibe Mamora - Legas
- Sunday Dare - Oyo
- Festus Keyamo - Delta
- Sharon Ikeazor - Anambra
- Sanata Tayo Alasoadura - Ondo
- Pauline Tallen - Filato
- Mustapha Buba Jedi Agba -
- Olamilekan Adegbite - Ogun
- Mohammed Dangyadi - Sokoto
- Abubakar Aliyu - Yobe
- Sale Mamman - Taraba
- Muhammed Mamood - Kaduna
- Uce Ogar - Abia
- Emeka Nwajuiba - Imo
- Akpa Udo
- Clement Abam
- Zubair Dada
- Adeniyi Adebayo - Ekiti
- Mohammed Abdullahi
- Osagie Ehenere
- Bashir Salihi Magashi - Kano
Tsoffin ministocin da suka dawo
- Babatunde Fashola - Tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje
- Rotimi Amaechi - Tsohon Ministan Sufuri
- Ogbonnaya Onu - Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha
- Adamu Adamu - Tsohon Ministan Ilimi
- Sanata Chris Ngige - Tsohon Ministan Kwadago H
- Hadi Sirika - Tsohon Karamin Ministan Sufurin Jiragen Sama
- Zainab Ahmad - Tsohuwar Ministar Kudi
- Lai Mohammed - Tsohon Ministan Watsa Labarai
- Musa Bello - Tsohon Minsitan Abuja
- Abubakar Malami - Tsohon Ministan Shari'a
- Sulaiman Adamu - Tsohon ministan ruwa
- Baba Shehuri - Borno







